Samira Khalil | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 20 century |
ƙasa | Siriya |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Yassin al-Haj Saleh (en) |
Karatu | |
Harsuna | Larabci |
Sana'a | |
Sana'a | Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Kyaututtuka |
gani
|
Mamba | Center for Documentation of Violations in Syria (en) |
Samira Khalil ( Larabci: سميرة الخليل ) yar gwagwarmaya ce daga yankin Homs na kasar Syria . Ta kasance a gidan yari na tsawon shekaru hudu, daga shekara ta alif Dari Tara da tamanin da bakwai 1987 zuwa shekara ta alif Dari Tara da casain da data 1991, saboda tai adawa da gwamnatin Bashar al-Assad a Syria . Ta bace a birnin Douma a ranar 9 ga watan Disamba, 2013, tare da masu fafutuka Razan Zeitouneh, Wael Hamada, da Nazem Hammadi . Ana kiran su " Douma 4 ".
Bayan kurkuku, Khalil ta gudanar da aikin buga littattafai . Sannan ta yi aiki da iyalan wadanda ake tsare da su . Ta kuma yi rubutu game da tsare mutane a Siriya. Kafin sace ta, ta yi aiki don taimaka wa mata a Douma don fara ƙananan ayyuka don samun kuɗi. Ta zauna a Douma don fara cibiyoyi biyu na mata.
Khalil da mijinta Yassin al-Haj Saleh sun kasance a cikin wani fim na Documentary mai suna Baladna Alraheeb (Kasarmu mai Muni). Fim ɗin ya kasance game da lokacin rayuwar su kafin sace Khalil a shekara ta 2013.
Khalil ta sami lambar yabo ta Petra Kelly daga Gidauniyar Heinrich Böll a cikin shekara ta 2014. Wannan don aikinta ne a Cibiyar Takaddun Takaddun Cin Hanci da Rashawa a kasar Siriya .