Samuel Ortom | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2015 - 29 Mayu 2023 ← Gabriel Suswam
14 ga Faburairu, 2014 - 15 ga Augusta, 2014 ← Stella Oduah
11 ga Yuli, 2011 - 25 Oktoba 2015 | |||||||
Rayuwa | |||||||
Cikakken suna | Samuel Ioraer Ortom | ||||||
Haihuwa | Jahar Benue, 23 ga Afirilu, 1961 (63 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Ƙabila | Tiv | ||||||
Harshen uwa | Harshen Tiv | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta | Jami'ar Ahmadu Bello | ||||||
Matakin karatu | Master in Public Administration (en) | ||||||
Harsuna |
Turanci Harshen Tiv Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa da ɗan kasuwa | ||||||
Kyaututtuka |
gani
| ||||||
Imani | |||||||
Addini | Kiristanci | ||||||
Jam'iyar siyasa | People's Democratic Party (en) |
Samuel Ioraer Ortom saurare; an haife shi ranar 23 ga watan Afrilu 1961) ɗan siyasan Najeriya ne, kuma ɗan kasuwa, mai gudanarwa kuma mai taimakon jama'a. Ya kasance karamin ministan kasuwanci da saka hannun jari a Najeriya a lokacin mulkin Goodluck Jonathan. An zabi Ortom gwamnan jihar Benue a matsayin dan jam’iyyar All Progressives Congress a shekarar 2015. An sake zaɓen sa a matsayin gwamna a ranar 29 ga watan Mayu 2019.[1][2][3]
An haifi Ortom a ranar 23 ga watan Afrilu 1961 a karamar hukumar Guma ta jihar Benue, Najeriya. Ya halarci makarantar firamare ta St. John's Gboko a shekarar 1970 amma ya koma St. Catherine's Primary School, Makurdi a shekarar 1974, inda ya kammala karatunsa na firamare a shekarar 1976. Cif Dr. Samuel Ioraer Ortom ya samu gurbin shiga makarantar sakandaren kasuwanci ta Idah, Idah a jihar Kogi a shekarar 1976.[4] Ya yi shekara biyu a makarantar kafin mahaifinsa ya yi ritaya a shekarar 1979 ya kawo karshen burinsa na kammala karatun sakandare saboda kudi. Ya zama kwararren direba.
Daga nan ya samu shaidar kammala karatu da kuma Diploma a fannin tallace-tallace. Ya yi rajista a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya kuma samu shaidar kammala karatun digiri na wucin gadi a shekarar 1995 da kuma Diploma a aikin jarida a 1998. Daga nan ya halarci Jami’ar Jihar Binuwai inda ya sami Difloma mai zurfi a fannin Gudanar da Ma’aikata a shekarar 2001 da kuma Digiri na biyu a fannin Gudanarwa a shekarar 2004. Ortom ya sami Ph.D, daga Jami'ar Commonwealth, Belize, ta hanyar koyan nesa wato distance learning.
Ortom ya yi aiki da jam’iyyun siyasa daban-daban a jihar Binuwai da suka haɗa da National Center Party of Nigeria a matsayin Sakataren Yaɗa Labarai na Jiha; Ma'ajin Jam'iyyar Jama'a (APP); da Sakataren Jiha da kuma Mataimakin Shugaban Jam’iyyar PDP na Jiha. Ya kuma taɓa zama Darakta mai kula da ayyuka na yakin neman zaɓen ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Benuwe a shekarar 2007 da kuma daraktan gudanarwa da dabaru na kungiyar yakin neman zaben shugaban kasa Goodluck/Sambo a shekarar 2011. Ya kasance mai binciken kuɗi na kasa na PDP kafin a naɗa shi a matsayin Ministan Tarayyar Najeriya a watan Yulin 2011.[5]
A watan Afrilun 2015, ya tsaya takarar gwamnan jihar Benue kuma ya yi nasara a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
A watan Yulin 2018, Ortom ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress sakamakon rikicin cikin gida na jam’iyyar.
A zaben gwamnan jihar Benue da aka gudanar a ranar 9 ga Maris 2019 da kuma ranar 23 ga watan Maris 2019, an sake zaben Ortom a matsayin Gwamna bayan da ya samu kuri'u 434,473 yayin da Emmanuel Jime na jam'iyyar All Progressive Congress ya samu kuri'u 345,155. Bayan zaɓen, Jime ya kalubalanci nasarar Ortom kuma ya shigar da kara a kan dalilan rashin bin ka’idojin dokar zabe, 2010 da aka yi wa kwaskwarima. A ranar 21 ga watan Junairu 2020 kotun koli ta tabbatar da zaben Samuel Ortom a matsayin gwamnan jihar Benue.
Ta hanyar kafa gidauniyar Oracle Business Limited, Ortom ya ware kudade a Asibitin St. Theresa, Asibitin Makurdi da Rahama, dake titin Gboko Road, Makurdi, domin jinyar ciwon cizon sauro da cizon maciji kyauta ga marasa lafiya. Gidauniyar ta kuma yi aiki don rage wa fursunonin wahalhalu, yayin da ta kuma bayar da dabaru daban-daban na koyon sana’o’i domin ingantacciyar hanyar shiga cikin al’umma. Makarantar Tuƙi ta Oracle wani shiri ne, wanda ke horar da ƙwararrun direbobi akai-akai.[6]
A yanzu haka yana da aure da ‘ya’ya ga matarsa Mrs. Eunice Erdoo Ortom.