Sarah Reng Ochekpe | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 4 Oktoba 1961 (63 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Nelson Ochekpe (en) |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello Digiri a kimiyya : Kimiyyar siyasa Jami'ar, Jos Master of Science (en) : public administration (en) |
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Addini | Kiristanci |
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Sarah Reng Ochekpe yar siyasa ce a Najeriya, kuma ta fito ne daga Jihar Filato. Ta kasance Ministar Albarkatun Ruwa daga (2011 zuwa 2015).
An haife Ochekpe a ranar 4 ga watan Oktoban 1961, ga dangin Ali Reng Madugben a garin Foron, wani yanki na ƙaramar hukumar Barikin Ladi ta Jihar Plateau. Ta yi digirinta na farko a Kimiyyar Siyasa daga Jami’ar Ahmadu Bello, sannan ta yi digiri na biyu a kan harkokin mulki daga Jami’ar Jos. Har ila yau, tana da digiri na biyu daga Kwalejin Kasuwanci na Aberdeen da Cibiyar Nazarin Aikin Jarida ta Najeriya .[1][2]
Ta kasance tana auren Farfesa Nelson Ochekpe daga ƙaramarOhukumar tukpo daga gJihar Benue. Shi farfesa ne a fannin kimiyyar harhada magunguna kuma Mataimakin Shugaban a Jami’ar Jos.[3]
Ochekpe ta riƙe mukamai da yawa a hukumar kula da wayar da kai ta ƙasa na (Najeriya), kafin a naɗa ta minista kenan. A lokacin da take cikin gwamnati, an lura da cewa ta kara imganta atakiansamar da ruwan sha ga 'yan Najeriya zuwa kashi( 0%) sannan kuma ta kirkira gyaran hanyoyin ruwa na roba wadanda suka rage ambaliyar ruwa, sannan ta samar da hanyoyin rage rashin aikin yi, ta hanyar samar da aiki.[4][5][6]A shekara ta (2017), ita da wasu mutane biyu an zarge su da halatta kudaden haram da hada baki da ya kai fam miliyan( 450).[7]