Seyi Edun | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Adeniyi Johnson (en) |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Obafemi Awolowo Tunyo Nursery and Primary School (en) |
Harsuna |
Yarbanci Turanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi da mai tsara fim |
Seyi Edun wanda aka fi sani da Ẹja nla, ƴar wasar Najeriya ce kuma mai shirya fina-finai.[1][2] Ta shahara da fim ɗinta na Eja nla, kuma ita ma matar jarumin finafinai ce, Adeniyi Johnson.[3][4][5]
Seyi Edun ƴar asalin Ayetoro Egbado ce a jihar Ogun. Ta yi karatun firamare da sakandare a Tunyo Nursery and Primary School da Anglican Girls Grammar School da ke Surelere, Legas. A shekarar 2011, ta sami digiri na farko a Jami'ar Obafemi Awolowo.[6]
Seyi Edun ta auri Adeniyi Johnson.[3][7][8]
Edun ta shiga harkar fim a shekarar 2009 ta hannun ƴar uwarta, wacce marubuciya ce. A wannan shekarar ta shiga makarantar wasan kwaikwayo ta Wisdom Caucus kuma ta kammala karatun a shekarar 2011. A shekarar da ta kammala karatun ta, ta fito da fim ɗinta na farko mai suna Ẹja nla.[6]
Ta fito a cikin fina-finai dake a ƙasa.[6]