Sinking Sands fim ne na wasan kwaikwayo na ƙasar Ghana na shekarar 2010, wanda Leila Djansi ta rubuta, shiryawa gami da bada Umarni, taurarin shirin sun haɗa da Jimmy Jean-Louis, Ama Abebrese, Emmanuel Yeboah A. da Yemi Blaq. Fim din an zabe shi sau tara (9) kuma ya lashe kyaututtuka 3 a shekara ta 2011 Africa Movie Academy Awards, ciki har da kyaututtuka na Best Screenplay & Best Makeup.[1][2][3][4][5][6][7][8]
Fim din ya ba da labarin wasu ma’aurata, Jimah da Pabi, waɗanda aurensu ya koma tashin hankali da cin zarafi yayin da Jimah ta samu matsala a wani rikicin cikin gida.[9]
Fim ɗin ya samu karbuwa sosai daga masu sukar fina-finan Afirka da yawa tare da NollywoodForever.com inda suka kammala da cewa "Fim mai ban mamaki da zan ba da shawarar daga ƙoƙon zuciyata. Fim mai kyau wanda ba ku yi ba, fim ɗin ya kasance mai ban sha'awa kuma a yaba masa, wasan kwaikwayo ya kasance a kan batu kamar yadda fim ɗin ya kasance."[10]
↑"Sinking Sands Comes To Nigeria". Leadership Newspaper. Abuja, Nigeria: Leadership Newspaper Group Limited. 27 February 2011. Archived from the original on 22 July 2011. Retrieved 10 March 2011.