![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2017 - District: Bunkpurugu Constituency (en) ![]() Election: 2016 Ghanaian general election (en) ![]()
7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017 District: Bunkpurugu Constituency (en) ![]() Election: 2012 Ghanaian general election (en) ![]() | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Ghana, 15 ga Yuli, 1968 (56 shekaru) | ||||
ƙasa | Ghana | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
University of Cape Coast Bachelor of Arts (en) ![]() ![]() | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a |
ɗan siyasa, manager (en) ![]() ![]() | ||||
Imani | |||||
Addini | Kiristanci | ||||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
Solomon Namliit Boar (An haifeshi ranar 15 ga watan Yulin,shekara ta alif ɗari tara da sittin da takwas 1968) ɗan siyasan Ghana ne kuma ɗan majalisar dokokin kasar Ghana. Mamba ne na Sabuwar Jam'iyyar Kishin Kasa, kuma Tsohon Ministan Yanki na sabuwar yankin Arewa maso Gabashin Ghana.[1]
An haifi Boar a ranar 15 ga watan Yuli, 1968. Ya fito ne daga garin Bunkpurugu da ke Arewacin ƙasar Ghana.[2]
Ya shiga Jami'ar Cape Coast, Ghana kuma ya yi digirinsa a fannin nazarin gudanarwa a shekara ta 2007.[2] Ya kuma halarci Jami'ar Kimiyya da Fasaha ta Kwame Nkrumah, inda ya kammala digirin sa, a fannin (Executive Master of Business Administration, CEMBA) a shekara ta 2012. [2]
A watan Maris na 2017, Shugaba Nana Akufo-Addo ya naɗa Boar ɗaya daga cikin ministoci mataimakan sa su goma, da za su kafa wani ɓangare na gwamnatinsa.[3][4][5] Kwamitin naɗi na majalisar dokokin Ghana ya tantance shi a cikin wannan watan.[6] Kwamitin ya amince da shi kuma aka miƙa sunansa ga shugaban majalisar domin ƙara amincewa daga babban zauren majalisar.[7]
Boar Kirista ne ( Baftisma). Yana da aure (da 'ya'ya biyar).[2]