Stella Omu | |||
---|---|---|---|
Mayu 1999 - Mayu 2003 - James Manager → District: Delta South | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 22 Disamba 1946 (77 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Stella Omu (an haife ta a ranar 22, ga watan Disamba shekarar 1946) ƴar siyasar Nijeriya ce wacce aka zaba a matsayin Sanata a karkashin jam'iyyar PDP a shekarar 1999, don yankin Delta ta Kudu na Sanata na Jihar Delta.[1]
Omu ƴar asalin Isoko ne. An haife ta a ranar 22, ga watan Disamba shekarar 1946. Mijinta ya yi ritaya Manjo-Janar Paul Omu, tsohon Gwamnan Soja na Kudu maso Gabashin Najeriya . Ita ce mahaifiyar 'yaya mata uku da maza uku. Ta kasance mataimakiyar Kwanturola Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Najeriya, kuma ta yi ritaya daga aikin gwamnati a matsayin Konturola na Hukumar Gidajen Yari . Ta kasance mamba a kwamitin raba iko da majalisar wakilai (1994-95).
An zaɓe ta a matsayin Sanata a ƙarƙashin jam'iyar PDP a shekara ta 1999, tana wakiltar yankin Delta ta Kudu. Ta ƙike muƙamin na kwamitoci a majalisarr.