![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
29 Mayu 2007 - 29 Mayu 2015 ← Ibrahim Saminu Turaki - Badaru Abubakar →
1999 - 2003 ← Ignatius Olisemeka (en) ![]() | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Birnin Kudu, 30 ga Augusta, 1948 (76 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Hausawa | ||||
Harshen uwa | Hausa | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Government College, Birnin Kudu Kwalejin Barewa | ||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya | ||||
Imani | |||||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Sule Lamido (An haife shi a ranar talatin 30 ga watan Augustan shekarar alif ɗari tara da arba,in da takwas miladiyya 1948) ya taɓa zama ministan harkokin wajen Nijeriya daga shekarar 1999 zuwa shekara ta alif dubu biyu da uku 2003[1]. Daga bisani ya nemi takara kuma aka zaɓe shi Gwamnan Jihar Jigawa a watan Afurilun shekarar dubu biyu da bakwai 2007. Dan Jam'iyar People's Democratic Party (PDP) ne, kuma ya nemi zaɓe a takara ta biyu a shekarar 2011. A shekarar 2015 an gurfanar da shi da ‘ya’yansa maza bisa zargin satar kuɗaɗen gwamnati da EFCC ta yi.[2][3][4][5][6]
Matarsa Amina Sule Lamiɗo an haife ta a shekarar 1973 a Hausari Quarters Maiduguri. Ta kasance ma’abociyar addini ce wadda hakan yasa bata ɓoye daga idon duniya ba. Ta yi makarantar Irshad Primary Islamiyya (1980-1986) sannan post primary Academic a Junior Arabic Secondry School Sumaila (1988-1991).[7]
Sule Lamido ya riƙe muƙamin ministan waje tsakanin 1999-2003. An zaɓe shi a matsayin gwamnan Jihar Jigawa a shekara ta 2007 an kuma sake zabarsa a shekarar 2011 zuwa 2015. sule lamido yayi shekara takwas yana mulkin gwamna a jahar jigawa, ƙarƙashin jam’iyar PDP kuma ya nemi takaran shugaban ƙasa a shekara ta 2019.