![]() | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||||
2 ga Maris, 2020 - 14 ga Augusta, 2023
3 ga Yuli, 2019 - 5 ga Faburairu, 2020 - Ruth Monteiro →
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | 5 ga Yuli, 1973 (51 shekaru) | ||||||
ƙasa | Guinea-Bissau | ||||||
Karatu | |||||||
Makaranta |
University of Lisbon (en) ![]() | ||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa |
Suzi Barbosa 'yar siyasa ce ta Bissau-Guinean, 'yar majalisa kuma mai gudanarwa na kwamitin 'yan majalisar mata na Guinea-Bissau.[1]
Barbosa mai ba da shawara ce ga shigar mata cikin harkokin siyasa na ƙasa na Guinea-Bissau. Ta kasance ɗaya daga cikin masu rajin kare hakkin mata a Guinea-Bissau a tsakanin mata daga yankin Bafatá da suka kaucewa kada kuri'a a zaɓe idan ba a saka mata a cikin jerin 'yan takara ba. Ta yi nuni da cewa, “Guinea-Bissau tana da yawan al’ummarta galibi mata ne, kuma abin bakin ciki ne ganin cewa ba su da damar da maza suke da su, musamman wajen yanke shawara, da a ce suna da halin da ƙasar ke ciki ta fuskar tattalin arziki da kwanciyar hankali da ya bambanta.”[2][1][2]
Ta kasance wakiliya a taron farko na Da'irar Mata ta Majalissar Dokoki ta ƙasa a birnin Quebec a cikin shekarar ta 2017, wanda ya kunshi 'yan siyasa daga ƙasashen Faransa, da suka taru don inganta karfin shugabannin mata na duniya.[3]
Tun daga shekarar 2016, ta kasance Sakatariyar Harkokin Hulɗa da Jama'a ta Ƙasashen Duniya a Guinea-Bissau.[4]
A ranar 3 ga watan Yuli, 2019, ta zama Ministar Harkokin Waje. [5]