Tafasa

Tafasa
Scientific classification
KingdomPlantae
OrderFabales (mul) Fabales
DangiFabaceae (mul) Fabaceae
TribeCassieae (en) Cassieae
GenusSenna (en) Senna
jinsi Senna tora
Roxb., 1832
tafasa tanada matukar mahimmanci ga lafiyar Dan Adam

Tafasa (wadda Linnaeus ta siffanta shi da Cassia tora a turance kenan) nau'in tsiro ne a cikin dangin Fabaceae da dangin Caesalpinioideae. A kimiyyance an samo sunanta daga sunan Sinhala tora (තෝර). Mafi yawa tana tsirowa ne a daji a yawancin wurare masu zafi kuma ana daukarta a matsayin ciyawa a wurare da yawa. Asalin yankin da tafasa ta fara bayyana yana cikin Amurka ta tsakiya. Akasarin sunanta da Ingilishi shine sickle senna ko sickle wild- sensitive -plant. Ana kuma kiranta da wasu sunayen gama gari sun haɗa da sickle pod, tora, coffee pod da foetid cassia. Tafasa na matukar kama da wata tsiro a China wadda kira da Chinese senna ko sickle pod, Senna obtusifolia.[1]

Tafasa

Bayani a Hausance

[gyara sashe | gyara masomin]

wadda muka sani a kasar Hausa wata karamar.

bishiya ce da ke da ganye launin kore da fure da kananan

‘ya’ya a jikinta. Ita dai wannan bishiyar ana samun ta a

wurare da dama a kasashen Afirka ciki har da Nijeriya

musamman a jihohin Arewa. A kasar Indiya masu maganin

Ayurbedic Herbal Medicines sun dauki lokaci mai tsawo

suna amfani da tafasa dan yin maganin wasu kebabbun

rashin lafiyoyi kamar haka: Maganin makanta ko matsalar da

ta shafi ta gani. A baya ga wannan matsala ta barazanar na

makanta, tafasa na kara lafiyar ido kama daga yara har zuwa

tsofaffi. Domin haka sai a tunga yin miyan tafasa ana ci a

abinci.

Wani bincike da wasu masana tsirran itatuwa suka yi sun

tabbatar da cewa Tafasa na maganin wasu cututtukan da ke

shafuwar babbar hanzanya da kuma taurin bahaya.

Amfanin Tafasa

[gyara sashe | gyara masomin]
  • Tafasa tana maganin zafin ciki da kuma wanke dattin ciki da ya cushe.
  • Tafasa tana rage kiba dan haka wannan wata damace ga masu tumbi wadanda ke bukatar rage nauyi, sai a nemi, ganyen tafasa a dake a tare da gero a yi gumba a dama a yi kunu a tunga sha.
  • Ana amfani da sayyun tafasa idan suka bushe sai a dake su koma gari dan maganin cizon maciji.
  • Ana amfani da garin ganyen tafasa dan warkar da gyambon ciki wato ulcer.
  • Tafasa na maganin tsutsotsin ciki.
  • Tafasa na maganin cututtukan fata kamar su kazzuwa da makero da kuma kuraje masu kaikayi ga jiki.
  • Tafasa na saukar da yawan zafin jiki da hauhawar jini.
  • Tafasa na dauke da sinadiri mai suna chrysophanic acid da kuma sinadirin anthrone masu kashe kwayar cuta ta fungi.
  • Ganyen tafasa na inganta lafiyar hanta.
  • Ana amfani da ganyen tafasa ga yara kanana masu fitar da hakora.
  • Ganyen tafasa na maganin zazzabi da ciwon gabobin jiki. Sai a nemo ganyen a tafasa a yi surace da ruwan ko a yi wanka da su da sanyin safiya ko yamma.
  • Ganyen tafasa na wanke wasu sinadirran da ke gurbata ciki.
  • Diyan tafasa na maganin cututtukan sanyi na tari da mura musamman ga wadanda basa jimirin sauyin yanayi kamar a lokacin sanyi.
  • Wanda ya ci wani abu ko ya sha wani abu da ke da alaka da guba zai iya yin amfani da garin diyan tafasa in sha Allahu take zai amaya da wannan gubar a cikin lokaci kuma ba za ta illatar da shi ba da amincewar Allah.
  • Ganyen tafasa na maganin malaria.
  • Ganyen tafasa na warkar da cututtukan jinni.
  • Ganyen tafasa na maganin cututtukan ciki.
  • Ana amfani da garin diyan tafasa a markade da mai sai a shafawa a rauni ko wata jimuwa ko kuma kunar wuta.
  • Mai fama da basir mai haifar da zubar jinni sai ya tafasa ganyen tafasa ya marmasa gishiri a ruwan ya rinka tsuguno a ciki na mintuna goma ko fiye a duk sanda ya je bahaya.
  • Mai fama da tari sai ya ya markade ganyen tafasa a ruwan zafi ya dunga sha.
  • Nauyi ko ciwon mara a lokacin al’ada sai a yi amfani da tafasa. Sai dai mai fama da gudawa ba zai sha tafasa ba.
  • Mace mai ciki ta kiyaye yanda ake amfani da tafasa.
  • Mai ciwon hanta shi ma ya kiyaye.
  • Ana amfani da ganye da ‘ya’yan don yin magani. Tafasa maganin laxative ne da FDA ta amince da shi. Ana amfani da shi don magance Ulcer da kuma Cushewar da Ciki Ana kuma amfani da Tafasa ( Senna ) don maganin ciwon Ciki (IBS), ciwon basir, da Rage Kiba.

shayin Tafasa yana dauke da anthraquinone, wanda aka sani da tasirin laxative mai ƙarfi. Wadannan anthraquinone kuma Yana da tasiri sosai a tsaftace hanji, wanda yake da kyau ba kawai don ba da tsarin narkewa Abinci ba. Sai dai a lura duk wadannan bayanan babu madogara zuwa yanzu! A saboda haka idan ba'a tabbatar da Ingancin wadannan abubuwan da aka ambata ba a sama, wadanda Tafasa takeyi to kar ayi amfani dashi.

  1. "Senna tora (L.) Roxb". Royal Botanic Gardens Kew. 1838. Retrieved 10 January 2024.