Tama | |
---|---|
Wikimedia disambiguation page (en) |
Tama ba Larabawa bane, Wata kabilar afrika ce dake zaune a gabashin Cadi da yammacin Sudan. Suna yaren Tama, yaren nilo-Sahara. Yawan su yakai mutane (200,000–300,000) kuma sunayin addinin musulinci ne. Mafi yawancin su manoma ne mazauna Amma wasu kuma makiyaya ne. A yakin farar hula na Chadi a shekarar (2005–2010) Kabilar Tama tayi rikicin kabilanci da kabilar Zaghawa.[1][2]