Tanimowo Ogunlesi

Tanimowo Ogunlesi
Rayuwa
Haihuwa Iperu (en) Fassara, 1908
ƙasa Najeriya
Mutuwa Jahar Ibadan, 2002
Karatu
Makaranta University of London (en) Fassara
Makarantar St Anne, Ibadan
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa, Mai kare hakkin mata da suffragist (en) Fassara
Muhimman ayyuka National Council of Women's Societies (en) Fassara

Tanimowo Ogunlesi (haihuwa a shekarar alif 1908, mutuwa a shekarar 2002)[1] ta kasance mai fafutikan kare hakkin mata a Najeriya kuma jagorar harkokin cigaban mata wato Women's Improvement League.[2]Tana daya daga cikin manyan jagori akan harkokin mata na wannan karni, sannan kuma tare da ita aka kafa kungiyar "National Council of Women Societies", daya daga cikin muhimman kungiyoyin mata na Najeriya.

Rayuwa da aiki

[gyara sashe | gyara masomin]

Tanimowo Ogunlesi ta halarci makarantan mata na Ibadan; Kudeti Girls School Ibadan. Ta halarci makarantar "United Missionary College (UMC)" don samun horon ilimin koyarwa. Itace mutum na farko da ta fara kafa makarantan kwana na yara (firamare) a birnin Ibadan, "Children Home School".

Ta zama shugabar majalisar kare hakkin mata ta farko a shekarar 1959.[3] Ta yi aiki sosai kan kare hakkin mata, ta hanyar nemawa mata 'yancin jefa kuri'a da kuma samun damar zuwa wuraren koyon ilimi, kamar dai sauran mata masu kishin kasa.

Ba ta cika damuwa game da mallakar gidaje ga jinsi maza a Najeriya ba. Ta kasance cikin wani gangami na habaka ilimin kimiyyar zamantakewa a Najeriya a yayin da ta bude makarantar horo na gida.[4][5]

  1. "OGUNLESI Gladys Tanimowo Titilola (Née Okunsanya)". 3 September 2020.
  2. Foreign Data". Jet : 2004. Jet Magazine (Johnson Publishing Company): 40. December 16, 1961. ISSN 0021-5996.
  3. http://news.biafranigeriaworld.com/archive/ngguardian/2003/feb/19/article18.html Archived 2007-09-27 at the Wayback Machine - 16k
  4. Karen Tranberg Hansen; African Encounters with Domesticity. Rutgers University Press, 1992. p. 131–133.
  5. "Hajo Sani (2001). Women and national development: the way forward. Spectrum Books. p. 32. ISBN 978-9-780-2928-29.