Terry G | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | jahar Lagos, 17 ga Maris, 1986 (38 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | singer-songwriter (en) |
Gabriel Oche Amanyi ⓘ (an haife shi ranar 17 ga Maris shekarar1986), wanda aka fi sani da sunansa Terry G, mawaƙi ne na Najeriya, marubuci kuma mai gudanarwa. An san shi sosai don yanayin sa tufafin da ya dace, haka-zalika dalilin wasu kalmomin acikin waƙoƙinsa kuma mai wuyar sha'ani.[1] Jaridar The Punch ta bayyana shi a matsayin "ɗaya daga cikin mawaƙan da suka fi ban mamaki a duniya", ita kuma Vanguard, da kuma gidan talabijin na Channels TV sun bayyana shi a matsayin "mawaƙin da ya fi kowa hauka a Najeriya".[2][3][4] A cikin 2013, ya saki kundi waƙoƙin sa na huɗu, mai suna: Book of Ginjah.
An haifi Gabriel Oche Amanyi, wanda aka fi sani da Terry G, a ranar 17 ga Maris, 1986, a Jihar Benuwe. Ranar haihuwar sa tayi dai-dai da ranar da aka haifi mahaifiyarsa. Ya fara rera waƙa a cikin mawaƙan cocin yankinsa.[1]
“Akpako Master”, kamar yadda ake kiransa, ya sami yabo sosai saboda irin kiɗan da yake da shi na musamman.
Ta hanyar waƙoƙinsa, ya yarda cewa yana amfani da ƙwayoyi da barasa.[5][6] A cikin watan Satumba na 2014, ya gaya wa Jane Augoye na Jaridar The Punch cewa ya daina shan miyagun ƙwayoyi.
Ya ambaci 2face Idibia a matsayin babban mashawarcinsa na kiɗa.[7]
Shekara | Suna | Mai bada umarni | Madogara |
---|---|---|---|
2016 | Nonsense | Alien and Lucas Reid | [10] |