Teshie | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | |||
Yankuna na Ghana | Yankin Greater Accra | |||
Former district of Ghana (en) | Ledzokuku-Krowor Municipal District (en) | |||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 182,145 (2010) | |||
Labarin ƙasa | ||||
Altitude (en) | 13 m |
Teshie birni ne na bakin teku da ke a gundumar Ledzokuku Municipal, gunduma a cikin Babban yankin Accra[1][2][3] na kudu maso gabashin ƙasar Ghana.[4] Teshie shine yanki na tara mafi yawan jama'a a ƙasar Ghana, mai yawan jama'a 171,875.[5]
Teshie yana mazaɓar Ledzokuku ƙarƙashin jagorancin Hon. Ben Ayiku, memba na jam'iyyar National Democratic Congress,[6] wanda ya gaji Hon. Dr Bernard Okoe Boye na Jam'iyyar New Patriotic Party (Ghana).[7]
Teshie na ɗaya daga cikin garuruwan jihar Ga mai cin gashin kansa, duk watan Agusta, garin na gudanar da Bikin Homowo.[8][9] An yi imanin cewa mutanen Teshie na asali sun fito ne daga La, wani gari da ke yammacin Teshie.
Ganuwar Augustaborg, wanda Danes suka gina a shekarar 1787, yana cikin Teshie kuma Burtaniya ta mamaye shi daga shekara ta 1850 zuwa 1957. An yi imanin cewa wurin na (Fort Augustaborg) da ke Teshie, na da shekaru 300 kamar a rahoton 2011.[9]
Garin dai na da ɗumbin al’adu daban-daban sakamakon tsarin dimokuradiyya da ci gaban ƙasar a halin yanzu.
Teshie ya tashi daga Lagon Kpeshie zuwa Teshie-Nungua Estates (mahaɗar farko) daga Gabas zuwa Yamma akan Titin Teshie. Birnin Teshie ya bunƙasa sosai, ya zama ɗaya daga cikin manyan garuruwa a Ghana.
An kuma san garin Teshie a matsayin gidan design coffin, wanda Seth Kane Kwei ya ƙirƙira a cikin shekara ta 1950s [10] kuma har yanzu ana ƙerawa a wurin ƙira na Kane Kwei Carpentry Workshop (wanda Eric Adjetey Anang ke gudanarwa) da kuma wasu masu fasaha da yawa. [11]
Tekun Labadi, ko kuma wanda aka fi sani da La Pleasure Beach, yana kusa da Teshie. Tekun ita ce bakin teku mafi yawan jama'a a gabar tekun Ghana. Wurin na ɗaya daga cikin ƴan rairayin bakin teku na Greater Accra kuma otal-otal na yankin ne, ke kula da shi.
Har ila yau, akwai wasu makarantu masu zaman kansu da ake gudanar da su, daga cikin su akwai; makarantar God's Way Preparatory School, Teshie St. John Schools, Makarantun Teshie St. John, Sunrise Preparatory & JHS, Nanna Mission Academy, Ford Schools Ltd.[19]
Faɗaɗa hanyar jigilar kaya biyu daga Barracks OTU zuwa Junction na Farko ya kasance a ƙarshen shekarun 1970s. [20]
Garin Teshie na amfani da tashar gabas na tsarin layin dogo na kasa.