The Guardian | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | takardar jarida |
Ƙasa | Najeriya |
Harshen amfani | Turanci |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1983 |
|
The Guardian jarida ce mai zaman kanta a Najeriya, wacce aka kafa a cikin shekara ta 1983, wacce jaridar Guardian Limited ta samar a Legas, Najeriya.[1]
Alex Ibru, ɗan kasuwa, da shi da Stanley Macebuh, babban ɗan jarida tare da jaridun Daily Times ne, suka kafa The Guardian a cikin shekara ta 1983. An kwafi samfurin jaridar daga ainihin jaridar The Guardian ta Burtaniya. The Guardian ta kasance majagaba wajen gabatar da aikin jarida mai inganci a Najeriya tare da ingantattun rahotanni.[2] An fara buga labaran jaridar ne, a ranar 22 ga watan Fabrairu, 1983 a matsayin wallafa labarai duk mako-mako, wato tana fitowa a duk ranar Lahadi. An fara buga labarai a kullun, a ranar 4 ga watan Yuli, 1983.[3]
A lokacin mulkin soja na gwamnatin Janar Muhammadu Buhari, an tura manema labarai da suka haɗa da; Tunde Thompson da Nduka Irabor a gidan yari a shekarar 1984 a ƙarƙashin doka mai lamba 4 ta 1984, wadda ta danne ƴancin aikin jarida.[4][5] A ranar 26 ga watan Agustan 1989 jaridar The Guardian ta buga wata doguwar wasika daga Dokta Bekolari Ransome-Kuti, mai fafutukar kare hakkin bil’adama, mai taken “Budaddiyar Wasika zuwa ga Shugaba Babangida”, inda ya soki abin da ya ke ganin na ƙara murkushe ƴancin fadin albarkacin baki da gwamnati ke yi.[6]
Mamallakin Jaridar Alex Ibru, ya tsallake rijiya da baya a yunƙurin kashe shi a lokacin mulkin soja na Janar Sani Abacha.[7] A ranar 2 ga Fabrairun 1996 aka harbi motarsa kuma aka kai wa Ibru hari. An garzaya da shi asibiti idanunsa na lumshewa. Bayan mutuwar Sani Abacha, ta ba zato ba tsammani a watan Yuni 1998, an fara shari'a akan ɗansa Mohammed Abacha da babban jami'in tsaro Major Hamza al-Mustapha . Daga karshe dai a watan Disambar 2010 wata babbar kotun Legas ta wanke waɗanda ake zargi da yunƙurin.[8][9]
Kamfanin Jaridar The Guardian mallakar wani memba a ƙungiyar ethnic minority ce. Jaridar ta kasance mai mutunta ra'ayin kowace kabila, al'ummar addini, jam'iyyar siyasa ko wata kungiya mai wani ra'ayi . Sai dai ana zargin jaridar da nuna kiyayya ga kabilar Ibo.[10]
Jaridar New York Times ta bayyana Guardian a shekarar 1988 a matsayin "jarida mafi daraja a Najeriya".[11]