Timidria | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | non-governmental organization (en) da Ƙungiyar kare hakkin dan'adam |
Masana'anta | international activities (en) |
Ƙasa | Nijar |
Mulki | |
Shugaba | Ilguilas Weila (en) |
Hedkwata | Niamey |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 1991 |
Timidria sunan wata kungiya ce mai zaman kanta, da aka kafa ta domin kare hakkin dan adam a kasar Nijar, wanda Ilguilas Weila ya kafa. Timidria an sadaukar da ita domin yaqi da aikin Bauta a kasar Nijar.[1][2]
An kafa Timidria a cikin shekarar alif dubu daya da dari tara da casa'in da daya 1991, kuma sunan yana nufin 'haɗin kai' a harshen Tamajaq. Gwamnatin Nijar ta musanta wanzuwar aikin bauta a kasar, amma kungiyoyin kare hakkin dan adam na kasa da kasa sun kiyasta yawan bayi a Nijar wadda sun kusan mutum 40,000.[3]
Hedikwatar Timidria tana cikin babban birnin Niamey na kasar Nijar, kuma kungiyar tana da ofisoshi a duk faɗin ƙasar, tana taimakawa bayi da suka tsere don gina sabuwar rayuwa cikin 'yanci.[4]