![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Lagos,, 1985 (39/40 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Titilope Sonuga, wanda aka fi sani da Titi Sonuga, ta kasance mawaƙiyar Najeriya ce, injiniya, kuma mai yin wasan kwaikwayo wadda ta rayu a tsakanin Legas da Edmonton, Kanada.
Titilope Sonuga an haife ta ne a Legas, Najeriya, ta koma Edmonton, Kanada, lokacin tana shekara 13. [1] Sonuga ta yi aiki na tsawon shekaru biyar a matsayin injiniya, ta yi amfani da lokacin da ta fi dacewa don bibiyar mawaƙa da kuma burin ta. [2]
Sonuga ta lashe kyautar Kungiyar marubutan Kanada ta shekarar 2011 wanda ke fitowa a Matsayin rubutun Marubuta, da kuma a watan Mayu na shekarar 2012. [3] Ta kafa tarihin zama mawakiya da ta fara kasancewa a rantsar da shugaba kasa a Najeriya, Ta kafa Rouge Poetry a Edmonton. A watan Mayun shekarar 2015 ta kasance mawaƙiya ta farko da ta fito a wurin bikin rantsar da shugaban ƙasar Najeriya. Ta buga tarin wakoki a shekarar 2016. Sonuga ta yi wannan bikin ne a cikin Wasannin Mawaka na kasa da kasa na Legas .
Banda waka, Sonuga ta nuna rawar takawa a cikin shirin fim, sannan ta bayyana a matsayin Eki a jerin shirye-shiryen NdaniTV na biyu Gidi Up tare da OC Ukeje, Deyemi Okanlawon, Somkele Iyamah da Ikechukwu Onunakuhttps . [4] Har ila yau, tana aiki a matsayin jakadan Intel na Kamfanin She Will Connect Program a fadin Najeriya.
A shekarar 2015 ta ba da sanarwar fara nauyinta ga mai daukar hoto Seun Williams.