Tukur Yusuf Buratai

Tukur Yusuf Buratai
Aliyu Muhammad Gusau

13 ga Yuli, 2015 - 26 ga Janairu, 2021 - Ibrahim Attahiru
military commander (en) Fassara

Mayu 2014 - ga Yuli, 2015
Rayuwa
Haihuwa Biu, 24 Nuwamba, 1960 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Babur
Karatu
Makaranta Jami'ar Maiduguri
Jami'ar Tsaron Nijeriya
Harsuna Turanci
Babur
Kanuri
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a soja
Aikin soja
Digiri lieutenant general (en) Fassara
Ya faɗaci Rikicin Boko Haram

Tukur Yusuf BurataiAbout this soundTukur Yusuf Buratai  Laftanar Janar din soja ne a Najeriya kuma shugaban sojojin kasan Najeriya ne a yanzu, matsayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi tun a 2015. An haife shi a garin Buratai dake karamar hukumar Biu ta jihar Borno, a ranar 24 ga watan Nuwamba a shekarar 1960. Don haka, Buratai ɗan asalin jihar Borno ne dake arewa maso gabashin Najeriya.

Ty Buratai sambisa forest 2017

Laftana Janar TY Buratai shi ne hafsan Sojoji na ashirin da shida 26 a tarayyar Najeriya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya naɗa a ranar 13 ga watan Juni na shekarar 2015

.

Burtai ya yi karatun Furamari a garinsu buratai, daga nan ne ya zarce zuwa Kwalejin Malaman Gwamnati dake garin Potiskum a jihar Yobe. A watan Junairu na shekarar 1981, Buratai ya halarci Nigerian Defence Academy dake Kaduna a matsayin ɗaya daga cikin membobi a shirin nan na ‘29 Regular Combatant Course (29R)’. Haka zalika, Burtai ya samu takardar shaidar kammala Jami’a, wato Digiri a fannin History daga Jami’ar Maiduguri. Kuma yana da Digiri a fannin Philosophy daga Jami’ar Bangladesh University of Professions dake garin Dhaka.

Kafin naɗinsa a matsayin hafsan Soji, Buratai shi ke jagorantar rundunar tsaro ta hadin–gwiwa wacce ke da hedikwata a birnin Ndjamena na kasar Chadi. Kasashen Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi da kuma Benin ne suka kafa rundunar domin yaki da ’yan ta’addan da ke yankinsu.

A baya dai, Janar Buratai ya yi aiki a matsayin Kwamandan runduna ta Biyu ta sojin Najeriya dake birnin Fatakwal na jihar Rivers, sannan ya taba zama Kwamandan makarantar horas da sojin kasa dake Jaji, a jihar Kaduna.

Tarihin sa da karatun sa

[gyara sashe | gyara masomin]
Tukur Yusuf Buratai

Janar Buratai an haifeshi a garin Buratai, karamar hukumar Biu ta jahar Borno. Mahaifinsa Yusuf Buratai ma tsohon soja ne na Royal West African Frontier Force da kuma Yakin duniya na biyu inda yayi yaki a kasar Burma. Buratai yayi karatunsa na firamare a garin Buratai daga nan kuma ya samu takarar shiga makarantar horar da malamai ta garin Potiskum dake jahar Yobe, inda ya kammala da kyakkyawab sakamako.

Shiga Aikin Soja

[gyara sashe | gyara masomin]
Buratai da wasu manyan mutane

A watana janairu na 1981, Buaratai ya shiga makarantar horar da sojoji dake garin Kaduna. Sakamakon gwaggwabar nasarar da ya samu ta kammalawa ne sai ya samu matsayin Laftanar na biyu a ranar 17 ga Disamba na 1983 a cikin Kuratan sojojin Najeriya. Buratai yayi digiri a fannin ilimin tarihi a jami'ar Maiduguri da kuma wani digirin a fannin falsafa daga jami'ar kwararru ta kasar Bangalidash wato Bangladesh University of Professionals, Dhaka. Ya kuma yi karatu a makaranatr National Defence college, Mirpur, duka a kasar ta Bangalidash.

Ya shiga bataliyar matasan sojoji ta 26 a garin Elele dake Fatakwal, sai kuma mai nazari na harkar soja cikin rundunar sojoji ta majalisar dinkin duniya a kasar Angola, daga baya kuma sai yakoma bataliyar sojojin tsaro a 26 a Lagos wato Lagosa Garroson command Camp. Laftanar Janar Buratai kuma ya rike mukamin mai tafiyarwa na gidan yankin jaha a Abuja; wato 82 Motoruzed Batalion; sai 81 Balation, Bakasi Penninsular; Army Headquaters Garrison, Abuja kafin daga baya kuma sai yazama daraktan ma'aikata a kwalejin horon mayan jami'an soja dake Jaji.

Babban Hafsan Sojin Najeriya Yusuf Buratai
Tukur Yusuf Buratai

Ya kuma rike makamai kamar haka; AHQ Army Policy and Plans, Abuja; Mataimakin Shugaban tsare tsare na al'amuran gudabarwa, HQ Infantry Centre Jaji. Yadai rike mukamai da dama a bangarori daban daban.

Ranakun da ya samu karin girma

[gyara sashe | gyara masomin]

Lambobin yabon daya samu

[gyara sashe | gyara masomin]