Tunde Idiagbon | |||||
---|---|---|---|---|---|
31 Disamba 1983 - 27 ga Augusta, 1985 ← Alex Ifeanyichukwu Ekwueme - Ebitu Ukiwe (en) →
ga Yuli, 1978 - Oktoba 1979 ← Mustapha Amin - Mohammed Goni → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Ilorin, 14 Satumba 1942 | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Ƙabila | Yaren Yarbawa | ||||
Harshen uwa | Yarbanci | ||||
Mutuwa | Ilorin, 24 ga Maris, 1999 | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Makarantar Sojan Najeriya Pakistan Military Academy (en) Jami'ar Tsaron Nijeriya | ||||
Harsuna |
Turanci Hausa Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Digiri | Janar |
Tunde Abdulbaki Idiagbon (an haifeshi ranar 14 ga watan Satumba, 1943) a Iloriin, jihar Kwara. Janar ne na Najeriya wanda ya yi aiki a matsayin Shugaban Ma’aikata na shida, Babban Hedikwatar Koli (Na Biyu) Karkashin Shugaban Kasa na Soja Janar Muhammadu Buhari daga shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da ukku 1983 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da biyar 1985. Ya kuma kasance jigo a gwamnatin mulkin sojan Najeriya a tsakanin shekarun alif dubu daya da dari tara da sittin da shida 1966 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da saba'in da tara 1979, inda ya kasance mai kula da harkokin soja na jihar Borno a karkashin gwamnatin mulkin soja ta Janar Olusegun Obasanjo.[1]
Ya halarci makarantar firamare ta United, Ilorin daga shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin 1950 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da biyu 1952 kuma Okesuna Senior Primary School, Ilorin, shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da ukku 1953 zuwa shekarar alif hamsin da bakwai 57. Ya yi karatunsa na sakandare a Makarantar Soja ta Najeriya, Zariya tsakanin shekarar alif dubu daya da dari tara da hamsin da takwas 1958 zuwa sittin da biyu 62. ya shiga makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NMTC). A watan Fabrairun shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da hudu 1964, kwalejin ta koma makarantar horas da sojoji ta Najeriya (NDA). Daga shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyu 1962 zuwa shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyar 1965, Idiagbon ya halarci Pakistan Military Academy , Kakul (PMA Kakul), Abbottabad, Pakistan, inda ya sami digiri na farko a fannin tattalin arziki.[2]
A shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyu 1962, Idiagbon ya shiga aikin sojan Najeriya inda Bayan isowarsa Najeriya daga Pakistan aka bashi mukamin Laftanar na biyu a watan Afrilun shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyar 1965. Ya kasance kwamandan kamfani, bataliya ta hudu daga watan Agusta shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da biyar 1965 zuwa watan Fabrairu shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da shida 1966. A shekarar alif dubu daya da dari tara da sittin da shida 1966 yayi kwas na junior Commander a jami’a.
Nigerian Defence Academy , Kaduna. Daga 1966 zuwa 1967 ya kuma yi aiki a matsayin jami'in leken asiri, Bataliya ta 4 da Janar Hafsan Soja, Leken Asiri na 3, a rukunin farko. Ya samu mukamin Laftanar a shekarar 1966. Ya yi yakin basasar Najeriya, sannan aka nada shi Kwamanda na Bataliya ta 20 daga Oktoba 1967 zuwa Fabrairu 1968. A 1968 ya samu mukamin kyaftin . Shi ne kwamandan Bataliya ta 125, daga 1968 zuwa 1970 - wani rukunin fada mai ban tsoro.<ref><https://dailypost.ng/2019/01/21/tunde-idiagbon-overthrown-1985-buhari//ref> A cikin 1970, an ba shi mukamin manyan jami'ai. An nada shi Brigade Major kuma mataimakin kwamanda, 33 Brigade daga watan Maris 1970 zuwa Maris 1971 da kuma kwamanda, 29 Brigade daga Maris 1971 zuwa Disamba 1972. A Janairu 1973 ya zama babban hafsan hafsoshi, Grade 1 kuma daga kuma, shugaban ma'aikata Babban Hedikwatar Sojoji. An kara masa girma zuwa Laftanar Kanar a shekarar 1974. An nada shi kwamandan birgediya 31 da 15 daga Agusta 1975 zuwa Agusta 1978. A 1976 Idiagbon ya wuce Kwalejin Command and Staff College da ke Quetta, Pakistan, don ci gaba da horar da sojoji. A watan Yuli 1978 ya samu mukamin Kanal. An naɗa shi a matsayin darektan ma’aikata da tsare-tsare, hedkwatar sojoji a watan Oktoba 1979. A watan Mayun 1980 ya samu mukamin birgediya-janar. A 1981, ya halarci National Institute for Policy and Strategic Studies, Kuru, Jos, a jihar Plateau, sannan a 1982 ya halarci International Defence Management Course, Naval Postgraduate School, US. Ya kasance sakataren soji na sojojin Najeriya daga 1981 zuwa 1983
Daga watan Agusta 1978 zuwa Oktoba 1979, Shugaban mulkin soja, Janar Obasanjo ya nada Idiagbon a matsayin shugaban mulkin soja (mukamin da ake kira gwamna) na jihar Borno, Najeriya. Shugaban Ma'aikata, Babban Hedikwatar Janar Muhammadu Buhari ya nada Idiagbon a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin tarayya daga 31 ga Disamba 1983 zuwa 27 ga watan Agusta 1985. An bayyana shi a matsayin kwararren soja, ya taka muhimmiyar rawa a matsayin abin da gwamnatin Buhari ta kafa a mulkin soja. Idiagbon ya samu mukamin Major-General a shekarar 1985.