Umaru Shehu

Umaru Shehu
mataimakin shugaban jami'a

Rayuwa
Haihuwa Maiduguri, 8 Disamba 1930
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Hausa
Mutuwa Maiduguri, 2 Oktoba 2023
Karatu
Harsuna Turanci
Hausa
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a Malami da Farfesa
Employers Jami'ar Najeriya, Nsukka
Jami'ar Ahmadu Bello
Kyaututtuka
Mamba Makarantar Kimiyya ta Najeriya

Umaru Shehu (An haife shi ne a ranar 8 ga watan Disamba, a shekarar 1930), ya kasan ce shi ne farfesa a likitancin Nijeriya kuma tsohon Mataimakin Shugaban Jami'ar Nijeriya, Nsukka. Ya kasance Farfesa Emeritus, lafiyar al'umma, Jami'ar Maiduguri kuma tsohon Shugaban Kwalejin Kimiyya ta Najeriya.

Farfesa Umaru ya sami digiri na farko na likitanci, MBBS daga Jami'ar London. Farfesa Umaru Shehu ba kawai shahararren farfesa ne a likitancin Najeriya ba, dattijo ne.[1][2]

A jami'ar Bayero, Kano, an nada shi Pro-kansila da kuma shugaban majalisar gudanarwa, daga a shekarar 1993-1996,[3] sannan kuma ya ninka matsayin Pro-kansila da shugaban kwamitin gudanarwa na jami'ar ta Lagos, daga shekarar 1996-1997.[4][5] Ya yi aiki a matsayin memba na kwamitoci da yawa, kansiloli, ɓangarori dakuma kwamitocin a matakin kasa da na duniya.

Umaru Shehu a cikin mutane

Farfesa Umaru Shehu ya kasance shugaban makarantun koyon aikin likitanci a Afirka, daga shekarar 1973-1975; kuma mai nazarin waje na kiwon lafiyar jama'a, jami'ar makarantar likitanci ta Ghana. Shine shugaban kwamitin gwamnoni na yanzu na kungiyar STOPAIDS; shugaban hukumar kula da cutar kanjamau ta ƙasa, (NACA)]. Ya kuma sami haɗin gwiwa na Cibiyar Nazarin ciwon Kansa.

  1. M.D.Aminu (7 September 2019). "Professor Umaru Shehu". Daily Trust (in Turanci). Retrieved 30 June 2023.
  2. "Professor Emeritus Umaru Shehu CFR". IHV NIGERIA.org (in Turanci). Retrieved 30 June 2023.[permanent dead link]
  3. "Popular Nigerian academic, Umaru Shehu, is dead". Premium Times. 2 October 2023. Retrieved 4 October 2023.
  4. Auyo, Aisha (18 August 2018). "Prof Umaru Shehu: life and times of Nigeria's foremost academic guru". Neptune Prime (in Turanci). Retrieved 30 June 2023.
  5. Babah, Chinedu (20 March 2017). "SHEHU, Prof. Emeritus Umaru". Biographical Legacy and Research Foundation (in Turanci). Retrieved 30 June 2023.