Umuchima ƙauye ne da ke kusa da birnin Owerri, a cikin ƙaramar hukumar Owerri ta yamma a jihar Imo, Najeriya. Tare da Ihiagwa, Eziobodo da Obinze, tana iyaka da Jami'ar Fasaha ta Tarayya, Owerri.