![]() | |||
---|---|---|---|
![]() | |||
6 ga Afirilu, 2018 - 15 ga Augusta, 2024 ← Claver Gatete (en) ![]() ![]() | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Ruwanda | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Rwanda University of Warsaw (en) ![]() ![]() | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai tattala arziki, malamin jami'a da Malami | ||
Mahalarcin
|
Uzziel Ndagijimana masanin tattalin arziki ne dan kasar Rwanda wanda ke rike da muƙamin ministan kuɗi da tsare-tsare a gwamnatin shugaba Paul Kagame tun daga shekarar 2018.[1][2]
Ndagijimana yana da digirin digirgir a (PhD, Economics), 1998 daga Jami'ar Warsaw da MSc. a fannin Ilimin tattalin arziki daga Warsaw School of Economics.Economics]].[3]
Ndagijimana ya fara aikinsa a matsayin malami a tsangayar tattalin arziki, kimiyyar zamantakewa, da gudanarwa a jami'ar ƙasa ta Rwanda a shekarar 1999. A shekara ta 2002, ya koma shugabanci na gwamnatin Rwanda.[4]
Ndagijimana ya zama shugaban Makarantar Kuɗi da Banki a Kigali, Rwanda, daga shekarun 2002 zuwa 2007 bayan haka ya zama mataimakin shugaban jami'ar kasar Rwanda daga shekarun 2007 zuwa 2011.[4][5]
Ndagijimana shi ne Babban Sakatare na Ma'aikatar Lafiya, Jamhuriyar Ruwanda, daga watan Mayu 2011 zuwa watan Yuli 2014. Ya kuma kasance Ƙaramin Minista mai kula da Tsare-Tsare Tattalin Arziki a Ma'aikatar Kuɗi da Tsare Tattalin Arziki (MINECOFIN).[2]
A yayin babban taron shekara-shekara na bankin Afreximbank a Abuja don tunawa da cika shekaru 25 da kafuwa, ministar kuɗin Najeriya Kemi Adeosun ta gaji Ndagijimana a matsayin shugaban hukumar bankin.[6]
A ranar 7 ga watan Afrilu, 2018, Shugaba Paul Kagame ya naɗa Ndagijimana a matsayin ministan kuɗi da tsare-tsare na Ruwanda.[1] Ndagijimana ya kuma taɓa zama shugaban kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki na shugaban ƙasar Rwanda.[4]