Varshini Prakash | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Massachusetts, |
ƙasa | Tarayyar Amurka |
Sana'a | |
Sana'a | Malamin yanayi |
Employers | Sunrise Movement (en) |
Varshini Prakash ita mai rajin kare yanayin ne kuma babbar darekta ce ta Sunrise Movement, kungiyar 501(c)(4) wacce ta kirkiro a shekara ta 2017.[1] An sanya ta a cikin jerin sunayen Time 100 na shekara ta 2019,[2] kuma ta samu lambar yabo ta Saliyo Club John Muir a shekarar 2019.[3]
Prakash ta fara sanin ilimin canjin yanayi ne lokacin da take 'yar shekara 11 a yayin da take kallon labarai game da Indian Ocean tsunamina shekarar 2004.[4][5] Dukda dai taso ta zama likita bayan girmanta.[4]
Prakash ta tafi kwaleji a Jami'ar Massachusetts Amherst inda ta fara shiryawa kan al'amuran da suka shafi yanayi.[4][5] Yayin da take can, ta zama jagora ga kamfen ɗin burbushin man fetur na makaranta. Prakash ta kuma yi aiki tare da wata kungiyar kasa, Fosil Fuel Divestment Student Network. A cikin shekarar 2017, shekara guda bayan ta kammala karatu, UMass Amherst ya zama na farko babba, jami'ar gwamnati da ta nitse.[4][6]
A cikin 2017, Prakash ta ƙaddamar da Sunrise Movement, ƙungiyar siyasa ta Amurka da matasa ke jagoranta da 501{c}{4} waɗanda ke ba da shawarar aiwatar da siyasa kan canjin yanayi, tare da wasu masu haɗin gwiwa guda bakwai.[4][7]
A cikin 2018, ta zama babban darektan Sunrise Movement bayan kungiyar ta shirya zanga-zangar mamaye ofishin kakakin majalisar wakilan Amurka Nancy Pelosi tana neman a kafa kwamitin aiki na majalisar don magance canjin yanayi.[4]
An sanya ta a cikin jerin sunayen Time 100 na 2019.[8]
A matsayin wani ɓangare na aikinta tare da Sunrise Movement, Prakash na ba da shawarwari akan harkoki day suka shafi fannin Green New Deal.[9] A shekarar 2020, kungiyar ta amince da dan majalisar dattijan Amurka Bernie Sanders a zaben fidda gwanin dan takarar shugaban kasa.[5] An ambaci Prakash a matsayin mai ba da shawara ga rundunar kula da yanayi ta Joe Biden a shekarar 2020.[9][10][11][12] Ita ma memba ce mai ba da shawara a kungiyar Climate Power 2020, kungiyar da ta hada da 'yan Democrats da masu fafutuka da ke ba da shawarar kara sha'awar masu jefa kuri'ar Amurkawa kan daukar matakin sauyin yanayi.[11]
Prakash ita ce editan edita na littafin Winning the Green New Deal:Why We Must, How We Can, fito da watan Agusta 2020.[13][14][15] Ta kuma kasance mai ba da gudummawa ga The New Possible: Visions of Our World Beyond Crisis.[16][17]