Victor Boniface

Victor Boniface
Rayuwa
Haihuwa Akure,, 23 Disamba 2000 (24 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
FK Bodø/Glimt (en) Fassara4 ga Maris, 2019-1 ga Augusta, 20224813
  Royale Union Saint-Gilloise (en) Fassara2 ga Augusta, 2022-21 ga Yuli, 2023379
  Ƙungiyar ƙwallon ƙafar ta Najeriya2023-50
  Bayer 04 Leverkusen (en) Fassara22 ga Yuli, 2023-2314
 
Muƙami ko ƙwarewa Ataka
Lamban wasa 22
Tsayi 1.89 m
Hoton dan kwallo boniface

Victor Okoh Boniface[1] (an haife shi ne ranar 23 ga watan Disamba, 2000)[2] ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na kasar Najeriya wanda ke buga wasa a matsayin ɗan gaba a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Bundesliga ta Bayer Leverkusen da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kasa ta Najeriya.

Sana'ar ƙungiya

[gyara sashe | gyara masomin]

A ranar 22 ga watan Yulin, shekarar 2023, Boniface ya rattaba hannu a kulob din Bundesliga na Bayer Leverkusen kan kwantiragi har zuwa shekarar 2028, kuma an sanya masa riga mai lamba 22.[3] Ya fara buga wasansa na farko a Bundesliga a matsayin dan wasa a ranar 19 ga Agusta, a wasan da suka doke RB Leipzig da ci 3–2 a gida.A mako mai zuwa, a ranar 26 ga watan Agusta, ya zira kwallayen sa na farko a Bundesliga ta hanyar zura kwallaye biyu a filin wasa na Borussia Park a wasan da suka doke Borussia Mönchengladbach da ci 3-0 a waje.

Sana'ar ƙasa

[gyara sashe | gyara masomin]
Victor Boniface

Boniface ya fara buga wa babbar tawagar kasar Najeriya wasa ne a ranar 10 ga watan Satumba,a shekarar 2023,Wanda ya kasance sauyi a minti na 64 ga Taiwo Awoniyi. Ya bayar da taimako a wannan wasan ga Samuel Chukwueze.

Rayuwar Sirri

[gyara sashe | gyara masomin]

Victor Boniface Kirista ne.