Victor Mbaoma | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | jahar Legas, 20 Oktoba 1996 (28 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya Harshen, Ibo | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | centre-forward (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 1.84 m |
Victor Mbaoma (an haife shi ranar 20 ga watan Oktoba 1996) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Najeriya wanda ke taka leda a FC Qizilqum, a matsayin Centre forward.[1]
An haife shi a Legas, Ifeanyi ya fara taka leda a Remo Stars FC, Akwa United da Enyimba FC Bayan zamansa a Remo Stars FC, ya koma kungiyar kwallon kafa ta Eyinmba a shekarar 2019 bayan Remo Stars ya fice daga gasar kwallon kafa ta Najeriya.
Victor yana daya daga cikin ‘yan wasan da suka fi zura kwallo a raga a gasar kuma hakan ya kai ga kiransa ga ‘yan wasan Najeriya. Ya ci wa kungiyarsa Eyinmba kwallaye 16 a wasanni 21.[2]
Daya daga cikin manyan abubuwan da ya fi daukar hankali a rayuwarsa shi ne kiransa da a ka yi a tawagar Super Eagles ta Najeriya a shekarar 2022 domin buga wasannin sada zumunci tsakanin Mexico da Ecuador a 2022.[3]
Ya buga wasansa na farko a duniya a Najeriya a shekarar 2022 a lokacin da ake fafatawa tsakanin Mexico da Ecuador.
FC Qizilqum Zarafshon ne ya bayyana Victor a watan Janairun 2023 bayan an rattaba hannu da shi daga kungiyar Mouloudia Club d'Alger.[4]
Kulob din Aljeriya, Mouloudia Club d'Alger ya sanya hannu kan yarjejeniyar shekaru biyu a watan Yuni, 2022.[5]