![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Nairobi, 22 ga Maris, 1980 (44 shekaru) |
ƙasa | Kenya |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Nairobi |
Harsuna |
Turanci Harshen Swahili Yaren Kikuyu |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, mawaƙi da ɗan kasuwa |
Rosemary Wahu Kagwi,[1] ƙwararriya wacce aka fi sani da sunan ta Wahu, mawaƙiya ce ta ƙasar Kenya, ƴar wasan kwaikwayo, kuma ƴar kasuwa.
An haife ta ranar 22 ga watan Maris a shekara ta alif dari tara da tamanin 1980 a birnin Nairobi. Wahu ta halarci makarantar firamare ta Hospital Hill kuma ta wuce makarantar Precious Blood High School, wacce ke a Riruta. Yayin da take makaranta, ta rubuta waƙarta ta farko.[2] Wahu tsohuwar abin koyi ce kuma ɗalibar Jami'ar Nairobi, wadda ta kammala karatun digiri a digiri na farko a fannin ilimin lissafi da sadarwa.[3]
Ta auri David Mathenge wanda aka fi sani da Nameless, wani mawaƙin Kenya wanda ya lashe lambar yabo. Suna da ƴaƴa mata 3. Ta sadaukar da babbar nasara ta kawo yau, "Sweet Love" ga ɗaya daga cikin ƴaƴanta (TUMI).
Samfuri:MTV Africa Music Awards for Best Male and Female Artists