ThetaHealing | |
---|---|
alternative medicine (en) da energy medicine (en) |
Warkar da Theta wani tsari ne na taimakon kai-da-kai, wanda Vianna Stibal ta samar da shi a shekara ta 1994 don a taimaka wa mutane su sauya wani abu da suka yi imani da shi a cikin ransu, wanda yake hana su cim ma burikansu na ɓangaren lafiya da tara dukiya da soyayya.[1][2]
Ana aiwatar da tsarin ThetaHealing ne ga mutum ɗaya shi kaɗai, da ake kira ‘aikin imani’, a wannan tsarin mai aiwatarwa yana zama ne da wanda yake yi wa magani shi da shi suna kallon juna ko ta wayar tarho. Haka kuma, ana iya amfani da tsarin a matsayin hanyar yi wa kai magani da gwada kai ta kullum-kullum da tace tunani.[3][4]
Hikimar ita ce wanda ake yi wa maganin zai iya ganowa ya kuma sauya abubuwan da ya yi imani da su, waɗanda suke can cikin ransa, da waɗanda ya gada da na matakin ruhi.[2][4]Manufar ita ce a inganta lafiya da walwalar mutum, kamar yadda Vianna ta faɗa, aikin imani yana ƙarfafa mana guiwa ta hanyar ba mu damar cirewa munanan tunani da sauya su da masu kyau waɗanda suke da amfani.’[5]
Kamar yadda Vianna Stibal ta bayyana, falsafar tsarin ThetaHealing ta ginu ne bisa Matakan Rayuwa Bakwai da suke ba da wani tsari da yake nuna muhimmancin cewa Mahalliccin Kowa Shi ne na mataki na bakwai, haka kuma an sifanta shi da cewa wani wuri ne na tatacciyar soyayya da basira.’[6][7]
Matakai Bakwai na rayuwa suna bayyana duniya ta zahiri da ta ruhi da yadda suke da alaƙa da motsin ƙwayoyin halittu. Mataki na bakwai shi ne makamashin rayuwa da yake halittar komai.[8]
Bugu da ƙari, manufar tsarin za ta dace da manufofin mafi yawan addinai.[9]
An ƙalubalanci falsafar ThetaHealing saboda yanayin da dangantakar da take da shi na imani.[10][11]