Webensenu | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 15 century "BCE" |
Mutuwa | unknown value |
Ƴan uwa | |
Mahaifi | Amenhotep II |
Yare | Eighteenth Dynasty of Egypt (en) |
Sana'a |
Webensenu tsohon yariman Masar ne na daular sha takwas. Shi ɗa ne ga Fir'auna Amenhotep II kuma ɗan'uwan fir'auna Thutmose IV.
An ambaci shi, tare da ɗan'uwansa Nedjem, a kan wani mutum-mutumi na Minmose, mai kula da ayyuka a Karnak. Ya mutu tun yana karami kuma ana iya binne shi a kabarin mahaifinsa, KV35, watakila ita ce mummy da aka ajiye tare da Tiye da Matarsa. An kuma gano tulunsa da shabtis a cikin kabarin. Mai yuwuwa mummy na nan, kuma hakan na nuni da cewa watakila ya rasu yana dan shekara goma.