Wicked Game[1] wani fim ne na ƙasar Masar da aka fitar a shekarar dubu daya da dari tara da cas,in da daya 1991.[2] Wanda tauraron fim ɗin shi ne Salah Zulfikar kuma Henry Barakat ne ya ba da umarni.[3][4][5][6]
Marubucin Riyad Kamel ya auri kyakkyawa mata mai suna Camelia duk da dangantakarta ta baya da Azmi, lauyarsa. Yayinda Azmi ta auri Manar, wanda shine sakataren Raiyad. Manar ya yi zargin cewa Azmi da Camellia sun dawo tare.[7][8][9][10] Ta yi rikodin tef ga Camelia tana roƙon Azmi ta kashe Manar da Riyad, don haka ta yi makirci don saukar da su.