![]() | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Cikakken suna | Luis Willis Alvés Furtado | ||||||||||||||||||
Haihuwa |
Ivry-sur-Seine (mul) ![]() | ||||||||||||||||||
ƙasa | Cabo Verde | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||
Tsayi | 182 cm |
Willis Alvés Furtado (an haife shi ranar 4 ga watan Satumba 1997) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin winger a ƙungiyar KTP ta Finland. An haife shi a Faransa, yana wakiltar tawagar kasar Cape Verde.
Furtado ya fara aikinsa a Faransa da Scotland kafin ya koma FC Masr a Masar.[1] Ya fara wasansa na farko tare da Masr a wasan Premier na Masar da ci 3-0 akan El Entag El Harby a ranar 22 ga watan Satumba 2020.[2]
A ranar 12 ga watan Fabrairu 2023, Furtado ya sanya hannu kan kwangilar shekara guda tare da KTP a Finland. [3]
An haifi Furtado a Faransa kuma dan asalin Cape Verde ne. An kira shi zuwa wakiltar Cape Verde don wasan sada zumunci a cikin watan Oktoba 2020.[4] Ya yi wasan sa na farko a Cape Verde a wasan sada zumunci da suka doke Andorra da ci 2-1 a ranar 7 ga watan Oktoba 2020.[5]