Wodage Zvadya | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | 7 Satumba 1973 (51 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Isra'ila | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | Dan wasan tsalle-tsalle | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
|
Wodage Zvadya (Ibrananci: ודג' זבדיה; an haife shi a ranar 7 ga watan Satumban 1973) ɗan wasan tseren nesa ne (long-distance runner) na Isra'ila wanda ya ƙware a tseren marathon.
Ya kasance dan kasar Habasha har zuwa shekarar 1991 lokacin da ya yi hijira zuwa Isra'ila. [1] Ya ci lambar azurfa a shekarar 2001 Summer Universiade.[2] Mafi kyawun wasanninsa sa a gasar cin kofin Turai ko Cin Kofin Duniya shine matsayi na 22 da yazo a gasar cin kofin Turai ta shekarar 2002. Ya kuma fafata a Gasar Cin Kofin Turai na shekara ta 2006 da Gasar Cin Kofin Duniya na shekarun 2005 da 2007 da 2009 da Gasar Cin Kofin Duniya na Half Marathon na shekarun 2001 da 2002 da 2005. [1]
Mafi kyawun lokacinsa na tsere shine 14:07.14 mintuna a cikin tseren mita 5000, wanda ya samu a watan Yuli 1996 a Hechtel; 29:38.88 mintuna a tseren mita 10,000 da aka samu a watan Mayu 1996 a Tel Aviv; 1:04:30 hours a Gasar Duniya ta Half marathon, da yayi nasara a wasan kakar Universiade ta shekarar 2001 a Birnin Beijing; da dakika 2:16:04 a tseren marathon, wanda aka samu a watan Janairun 2004 a Tiberias.
Shekara | Gasa | Wuri | Matsayi | Taron | Bayanan kula |
---|---|---|---|---|---|
Representing Samfuri:ISR | |||||
1999 | Universiade | Palma de Mallorca, Spain | 10th | Half marathon | 1:06:17 |
2001 | Universiade | Beijing, PR China | 2nd | Half marathon | 1:04:30 |
2006 | European Championships | Gothenburg, Sweden | 34th | Marathon | 2:24:52 |
2007 | World Championships | Osaka, Japan | 34th | Marathon | 2:29:21 |