Yankuba Ceesay | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Serekunda (en) , 26 ga Yuni, 1984 (40 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Gambiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 7 |
Yankuba Ceesay (an haife shi a ranar 26 ga watan Yunin shekarar 1984), wanda kuma aka fi sani da Maal, ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Gambia ( yana buga wasa a matsayin dan wasan tsakiya). Yanzu ya zama kocin kulob ɗin Kastrup Boldklub (Denmark).
Lokacin da Ceesay ya koma kulob ɗin Alianza Atlético na Peru, ya zama dan Gambia na farko da ya fara buga wasan ƙwallon ƙafa a Latin Amurka. [1] Ya kuma yi ɗan taƙaitaccen gwaji tare da Walsall FC a cikin watan Janairu 2008. [2] A shekara ta 2008, ya koma kulob din Degerfors IF na Sweden, kuma a karon farko ya wakilci tawagar kwallon kafar Gambia a wasan da suka yi da Senegal. [3]
A ranar 7 ga watan Maris 2012, an sanar da cewa ya sanya hannu kan kwangilar shekaru biyu tare da Estonia Meistriliga JK Nõmme Kalju.[4] Ya fara buga gasar lig a kulob din a ranar 10 ga watan Maris ɗin shekarar 2012, a wasan da aka tashi babu ci da abokan hamayyar birnin FC Levadia Tallinn.[5] Ya yi gwaji tare da kulob ɗin Charlton Athletic da Leyton Orient a cikin watan Janairu 2013.[6] A ranar 23 ga watan Yulin 2013, ya zura kwallo ta farko a Kalju a gasar zakarun Turai ta UEFA Champions League, kwallayen bude gasar a ci 2-1 da Ƙungiyar HJK ta Finland. [7] Ya bar kungiyar ne bayan kakar wasa ta 2013, lokacin da kwantiraginsa na shekaru biyu ya kare. [8]