![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ogun, 29 ga Janairu, 1960 (64 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Makaranta |
Jami'ar Obafemi Awolowo Jami'ar jahar Lagos |
Matakin karatu |
Digiri master's degree (en) ![]() |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm2103287 |
Yemi Shodimu (an haife shi a ranar 29 ga watan Janairu a shekara ta 1960) ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya , mai gabatar da shirye-shiryen talabijin, darekta kuma mai shirya fina-finai.[1][2]
An haife shi a Abeokuta babban birnin jihar Ogun kudu maso yammacin Najeriya.[3] Ya yi rayuwar kuruciyarsa ne a Abeokuta a fadar Alake na Egbaland inda ya ga al'adun Yarabawa.[4] Ya halarci Jami'ar Obafemi Awolowo inda ya sami digiri na farko a fannin fasaha (BA) a fannin fasaha sannan ya wuce Jami'ar Legas inda ya sami digiri na biyu a fannin sadarwa (Mass communication).[5]
Ya fara aikin wasan kwaikwayo ne a shekarar, 1976, a wannan shekarar ne ya fito a wani fim mai suna Village Head Master. An san shi da rawar jagoran shiri da ya taka, Ajani in Oleku, fim din Tunde Kelani ya bayar da umarni.[6] A cikin shekara ta, 2018, an sanya shi a matsayin mai gabatar da shirin wasan kwaikwayo na satirical mai suna Isale Eko.[7]