Yusupha Yaffa

Yusupha Yaffa
Rayuwa
Haihuwa Serekunda (en) Fassara, 31 Disamba 1996 (28 shekaru)
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
 

Yusupha Yaffa dan wasan kwallon kafa ne dan kasar Gambia wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan gaba.

A matsayin sa na matashin ɗan wasan, Yaffa ya shiga makarantar matasa ta Italiyan Serie A Milan.[1] Kafin rabin kaka ta biyu 2014–15, Yaffa ya shiga makarantar matasa ta Eintracht Frankfurt a Bundesliga ta Jamus. [2] A cikin shekarar 2015, ya rattaba hannu a kulob na biyar na Jamus MSV Duisburg II. [3]

Kafin rabin kaka ta biyu na shekarar 2021–22, Yaffa ya rattaba hannu a kulob ɗin Tsarsko Selo a Top flight Bulgaria bayan gwaji ga tawagar Poland Korona Kielce. [4] A ranar 25 ga watan Fabrairu 2022, ya fara buga wasana sa na farko a kulob ɗin Tsarsko Selo, inda sukayi rashin nasara da ci 0 – 1 a karawar su da ƙungiyar Lokomotiv (Plovdiv). [5] A ranar 21 ga watan Mayu, 2022, a wasan karshe na kakar wasa ta bana, Tsarsko selo ta samu fanareti wanda zai iya kawo musu nasara da kuma ceto kungiyar daga faduwa. Yaffa ya yanke shawarar daukar bugun daga kai sai mai tsaron gida duk da cewa Martin Kavdanski shi ne mai cin bugun daga kai sai mai tsaron gida. Yaffa yana shirye ya dauki fenariti lokacin da mai kungiyar, Stoyne Manolov, ya shiga filin wasa kuma ya yi fada da shi. Ya bar filin wasa kuma Kavdanski ya ci bugun daga kai sai mai tsaron gida, amma bai samu ba kuma kungiyar ta koma mataki na uku. [6]

  1. "Yusupha Yaffa 'lied about his age when joining AC Milan' after Italian authorities claim he is 28, not 19" . independent.co.uk. Archived from the original on 2022-05-07.
  2. "Vorwurf der Vergewaltigung gegen Frankfurts Yaffa" . welt.de.
  3. "MSV-U23 verpflichtet Angreifer Yusupha Yaffa" . msv-duisburg.de.
  4. "Царско сели привлече Юсуфа Яфа" . 7dnisport.bg.
  5. Yusupha Yaffa at Soccerway
  6. Невиждан панаир в Царско село! Стойне Манолов нахлу на терена и налетя на бой на свой футболист

Hanyoyin haɗi na waje

[gyara sashe | gyara masomin]