Zeinat Sedki | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Misra, 4 Mayu 1912 |
ƙasa | Misra |
Harshen uwa | Egyptian Arabic (en) |
Mutuwa | Kairo, 2 ga Maris, 1978 |
Karatu | |
Harsuna | Egyptian Arabic (en) |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm0781323 |
Zeinat Sedki (4 ga Mayu, 1912 - 2 ga Maris, 1978) ƴar wasan kwaikwayo ce kuma 'yar wasan ban dariya ta ƙasar Masar.[1] Ta kasance ɗaya daga cikin mata masu fara wasan kwaikwayo a cikin fina-finai na Masar tare da Mary Mounib da Widad Hamdi.[2]
An haifi Zeinat Sedki Zeinab Mohamed Mosaad ranar 4 ga watan Mayu, 1912 a Alexandria, Misira. Ta auri wani mutumin da ya girme ta da shekaru 15 bayan mahaifinta ya tilasta mata barin makaranta. Ta sake aure bayan shekara guda. Bayan rasuwar mahaifinta, ta fara aikinta a matsayin ƴar rawa, kuma ta shiga ƙungiyar masu fasaha a farkon shekarun 1930. Ta gudu daga gida kuma ta shiga ƙungiyar wasan kwaikwayo ta wasan kwaikwayo da Naguib el-Rihani ya kafa inda ta yi wasan kwaikwayon shirin ya shahara, daga cikinsu akwai The Egyptian Pound (el Guineih el Masrî) a 1931. -Rihani ya ba ta sunan Zeinat Sedki maimakon sunan haihuwarta Zeinab Mohamed Saad.
Ta yi fim ɗinta na farko a fim ɗin 1934 na Mario Volpe The Accusation. Ta ba da gudummawar da ta samu ga fim ɗin "His Highness Wants to Marry" (1936). A cikin wannan fim ɗin, ta taka rawaa matsayin wata yarinya daga ƙauye. Daga baya za ta ci gaba da taka wanna rawar a kan a cikin wasan kwaikwayo na wasan kwaikwayo wanda Naguib el-Rihani da Badie Khairy suka rubuta. A ƙarshen aikinta, ta fara samun matsalolin kuɗi kuma ta fara sayar da kayan daki-(furniture) ɗinta don biyan kuɗin da ta kashe. A shekara ta 1976, tsohon shugaban ƙasar Masar Mohamed Anwar el-Sadat ya ba ta lambar yabo a The Art Feast kuma ya ba ta fansho na musamman.[3]