![]() | |
---|---|
Bayanai | |
Iri | kamfani |
Masana'anta | banki |
Aiki | |
Kayayyaki | |
Mulki | |
Hedkwata | Victoria Island, Lagos |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 2005 |
Dissolved | 5 ga Augusta, 2011 |
bankphb.com |
Ƙungiyar Bankin PHB ko (Platinum Habib Bank Group) a turance, ƙungiya ce dake bayar da hidimar na kuɗi a Afirka ta Yamma da Gabashin Afirka. Hedikwatar kungiyar ta kasance a tsibirin Victoria Island a Legas, Najeriya, tare da rassa a Najeriya, Gambia, Laberiya, Saliyo da Uganda. Bankin PHB Group yana ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin bankunan ajiye kuɗi a Afirka, tare da kiyasin tushen kadarorin da ya haura dalar Amurka biliyan 3.6, ya zuwa Disamba 2009.[1]
Membobin Kamfanin na Rukunin Bankin PHB sun haɗa da:[2]
A ranar 5 ga Agusta, 2011, Babban Bankin Najeriya ya soke lasisin aiki na BankPHB, tare da na Afribank da Spring Bank, saboda ba sun gaza mayar da jarin su kafin ranar 30 ga watan Satumban, 2011 na wa'adin da aka basu[3]
An kafa Keystone Bank Limited[4] a ranar 5 ga Agustan 2011, ta hanyar karbe dukkan kadarorin (ciki har da rassa) da kuma bashin bankin PHB wanda suka shude a yanzu, wanda aka soke lasisin kasuwancinta a rana guda.
Bayan soke lasisin banki tare da karbe iko daga bankin PHB, Nigeria Stock Exchange ta dakatar da hannun jarin kamfanin daga karshe kuma aka soke shi a ranar 5 ga Satumba, 2011.[5]