Alexander Djiku | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Montpellier, 9 ga Augusta, 1994 (30 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa |
Faransa Ghana | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Faransanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 74 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 182 cm |

Alexander Kwabena Baidoo Djiku, (an haife shi a ranar 9 ga watan Agusta shekara ta alif 1994) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya ga kulob ɗin Strasbourg na Ligue 1. An haife shi a Faransa, yana wakiltar tawagar kasar Ghana.[1]
Djiku ya yi aiki a matsayin matashi a Bastia. Ya buga ma kungiyar wasa har zuwa shekarar 2014, inda aka kara masa girma zuwa babban kungiyar. Bayan ya shafe shekaru uku a kulob din, ya koma Caen. Djiku ya fara buga wasansa na farko a wasan Coupe de la Ligue da Évian a watan Disamba 2013.[2] [3]
A ranar 11 ga Yuli 2017, ya koma Stade Malherbe Caen ta Ligue 1 kan kwantiragin shekaru hudu. Strasbourg ne ta saye shi a lokacin rani na 2019.[4]
Djiku dan asalin Ghana ne da kuma Faransa. Ya yi karo da manyan ‘yan wasan Ghana a wasan sada zumunci da Mali ta doke su da ci 3-0 a ranar 9 ga Oktoba 2020.[5] Ya buga wa Ghana wasa na biyu da Qatar a ranar 12 ga Oktoba 2020 inda ya taka rawar gani. Wasan na uku na Djiku ya zo ne lokacin da sabon kocin Black Stars ya ba shi damar fara wasan da Zimbabwe a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya inda Ghana ta ci 3-1.[6] Ya kasance yana cikin tawagar Ghana a gasar cin kofin kasashen Afrika na 2021 a Kamaru.