Ali Nuhu | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Ali Nuhu Mohammed |
Haihuwa | Maiduguri, 15 ga Maris, 1974 (50 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Mazauni | jahar Kano |
Harshen uwa |
Hausa Harshen Waja |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar, Jos |
Matakin karatu |
Digiri Bachelor of Arts (en) |
Harsuna |
Turanci Hausa Larabci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, darakta, mai tsara fim da marubin wasannin kwaykwayo |
Kyaututtuka |
gani
|
Imani | |
Addini | Musulunci |
IMDb | nm2683171 |
alinuhu.net |
Ali Nuhu Mohammed An haifi Ali Nuhu a ranar 15 ga watan Maris shekarar alif, 1974 a Maiduguri, Jihar Borno, ya girma a jihar Kano, iyayensa ƴan Balanga ne a jihar Gombe dake arewacin Nigeriya.
Ali Nuhu ya fito daga kabilar Tangale Waja , cikakken sunan mahaifinsa Nuhu Poloma wanda dan asalin jihar Gombe ne.
Ali ya girma a hannun mahaifiyar sa a jihar Kano, mahaifiyar sa ta rasu a shekarar 1999 shi kuma mahaifinsa ya rasu a shekara ta 2020. Ali Nuhu jarumine a harkar fina finai,sannan marubucine,mai bada umarni kuma furodusa ne a masana,antar shirya finafinai ta kannywood da Nollywood. Sannan kuma yakan yi rawa a wasu fina-finai.
Ali Nuhu yana fina-finan sa cikin harshen Hausa da turanci, sannan kuma yana cikin manyan jaruman da suka kafa masana'antar shirya finafinai ta kannywood.
Shekarun sa 49, ya kuma karanci geography a jami'ar Jos wato University of Jos a turance.
Mutane suna masa inkiya da "sarki Ali Nuhu/ King of kannywood, wanda a ƙalla zuwa yanzu ya fito a finafina sama da 500+ wanda ya samu lambobin yabo da dama. Ko a wannan shekara saida ya samu lambar yabon "Best actor award in the Nollywood Europe Golden Award (NEGA 2023)".
Ya fara harkar finafinai tun a shekarar 1999 wato shekarar da mahaifiyar sa ta rasu da wani fim mai taken "ABIN SIRRI NE" ya kuma fito a finafinan masana'antar shirya finafinai ta kudanci najeriya NOLLYWOOD irin su Tout too, The Ghost, The Millions and Diamonds in the Sky, da dai sauransu.
Jarumin yana da mata daya da yara biyu Ahmad da fatima.
A shekarar 2024 shugaban kasar Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban na masana'antar fina-finai ta Najeriya gaba daya.
An haifi Ali Nuhu Muhammad a Maiduguri, jihar Borno, a arewa maso gabashin Najeriya. Mahaifinsa Nuhu Poloma daga Balanga gari Jihar Gombe dake a ariwacin najeriya da mahaifiyarsa, da Fatima Karderam Digema daga Bama gidan gwamnatin jihar Borno. Ya girma a Jos da Kano.[1]
ali nuhu yanada mata daya da Yara guda biyu Ahmad Ali nuhu da Fatima Ali nuhu.
Ali ya yi karatu a Jami'ar Jos, Bayan karatun sakandare, ya sami digiri na farko a fannin ilimin na fasaha daga Jami'ar Jos. Yayi bautar kasa a Ibadan da ke jihar Oyo. Daga baya ya halarci Jami'ar Kudancin Kalifoniya don yayi kwas a fagen shirya fina-finai da fasahar sinima.[2]
Ali Nuhu ya fara fitowa a fim ne a shekarar ta 1999 mai suna “Abin sirri ne”. An fi saninsa da rawar da yake takawa a "Sangaya" wanda ya zama dayan finafinan Hausa da suka fi samun kudi a lokacin. Ali Nuhu ya fito a fina-finai da dama, wadanda suka hada da Azal, Jarumin Maza, da Stinda a matsayin fitaccen Jarumi a wajen bayar da gudummuwa a yayin bikin bayar da kyaututtuka na African Movie Academy a (2007). A shekarar ta 2019, Ali Nuhu ya yi bikin cikarsa shekaru 20 a masana'antar nishadantarwa. Ya fito a fina-finai kusan dari biyar (500).[3]
A shekarar 2024 shugaban Najeriya Bola Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban hukumar kula da fina-finai ta Najeriya.[4]
inda akayi ittifaki akan yana da mabiya a Twitter sama da mutane dubu dari da arba'in 140,000 da kuma mabiya a Facebook sama da mutane dubu uku 3,000,000 da kuma wasu a shafin Instagram sama da milyan mutane dubu dari 1,000,000.[5][6]
(BT) na nufin Ba Tabbas, ma'ana babu tabbacin kwanan wata da shekarar da fim din ya fita. Yayin da akwai wasu kuma da ake da tabbacin kwanan watan fitar su.
Fim | ↑ Shekara | Fim | Shekara |
---|---|---|---|
Abaya | BT | Alhini | BT |
Abin Sirri Ne | 1998 | Ali | BT |
Alhini | BT | Alkebba | BT |
Ali | BT | ||
Alkebba | BT | ||
Ambato | BT | ||
Aska Tara | BT | ||
Zuwa Da Kai | BT | ||
Uwar Miji | BT | ||
'Ya 'Ya Na | BT | ||
Ina Miji Na? | BT | ||
Gambiza | BT | ||
Namijin Duniya | BT | ||
Dama da Hauni | BT | ||
Ga Fili Ga Mai Doki | BT | ||
Masu Aji | BT | ||
Zo Mu Zauna | BT | ||
Mashi | 2003 | ||
Gida da Waje | BT | ||
Yanayi | BT | ||
Farin Wata | BT | ||
Sakayya | 1998 | ||
Harafin So | BT | ||
Zuciya Ko Ruhi | BT | ||
Sangaya | 2000 | ||
JIGAL | 2002 | ||
Bashin Gaba | BT | ||
Mai Gadon Zinare | BT | ||
Ragowar Yaki | BT | ||
Kishin Mata | BT | ||
Jurwaye | BT | ||
Fitilar Dare | BT | ||
Rana da Wata | BT | ||
Umarnin Uwa | BT | ||
Gadan Ga | BT | ||
Sabon Shafi | BT | ||
Hawan Girma | BT | ||
Khalid | BT | ||
Maraichi | BT | ||
Har Abada | BT | ||
Qiyasi | BT | ||
Shamsiyya | BT | ||
Tawakkali | BT | ||
Raliya | BT | ||
Maryam Diyana | BT | ||
Rawani | BT | ||
Ban Ga Masoyi Ba | BT | ||
Gidan Iko | BT | ||
Zamba | BT | ||
Kamilalla | BT | ||
Nazari | BT | ||
Garinmu da Zafi (Dawo-Dawo) | BT | ||
Bilal | BT | ||
Mujadala | BT | ||
Bahaushiya | BT | ||
Rariya | 2017 | ||
Dangin Miji | 2017 | ||
Ba Tabbas | 2017 | ||
Mansoor | 2017 | ||
Zuciya Da Hawaye | 2017 | ||
Wacece Sarauniya? | 2017 | ||
Jarumta | 2016 | ||
Mu'amalat | 2016 | ||
Dattijo | 2016 | ||
Shinaz | 2016 | ||
Igiyar Zato | 2016 | ||
Halacci | 2015 | ||
'Yar Tasha | 2015 | ||
Wutar Gaba | 2015 | ||
Bani Bake | 2015 | ||
Gamu Nan Dai | 2015 | ||
Uba da 'Da | 2015 | ||
Baya da Kura | 2015 | ||
Ba'asi | 2015 | ||
Sallamar So | 2015 | ||
Kurman Allo | 2015 | ||
Nasibi | 2015 | ||
Hanyar Kano | 2014 | ||
Sirrin Da Ke Raina | 2014 | ||
Mai Dalilin Aure (Match Maker) | 2014 | ||
Jinin Jiki Na | 2014 | ||
Garbati | 2014 | ||
'Ya daga Allah | 2014 | ||
Idan Hakane | 2014 | ||
Kanin Miji | 2014 | ||
Mati da Lado | 2014 | ||
Sai a Lahira | 2014 | ||
Munafikin Mata | 2014 | ||
Duniyar Nan | 2014 | ||
So Aljannar Duniya | 2014 | ||
Hujja | 2014 | ||
Hakkin Miji | 2014 | ||
Andamali | 2013 | ||
Dakin Amarya | 2013 | ||
Nadawo Gareki | 2013 | ||
Wani Gari | 2013 | ||
Da Kishiyar Gida | 2013 | ||
Haske | 2013 | ||
Lamiraj | 2013 | ||
Jarumin Maza | 2013 | ||
Fari Da Baki | 2013 | ||
Zuri'a | 2013 | ||
Mai Jego | 2013 | ||
Mai Farin Jini | 2013 | ||
Halisa | 2013 | ||
Matar Jami'a | 2013 | ||
Kudi A Duhu | 2013 | ||
Madubin Dubawa | 2012 | ||
Gani Gaka | 2012 | ||
Wani Hanin | 2012 | ||
Kudi A Duhu | 2012 | ||
Son Zuciya | 2012 | ||
Dan Marayan Zaki | 2012 | ||
Kara da Kiyashi | 2012 | ||
Rai Dai | 2012 | ||
Hubbi | 2012 | ||
Bazan Barki Ba | 2012 | ||
Son Mai So | 2012 | ||
Blood and Henna | 2012 | ||
Maza Da Mata | 2012 | ||
Noor (The Light) | 2012 | ||
Talatu | 2012 | ||
Kona Gari | 2012 | ||
Adamsy | 2011 | ||
Alhaki Kwikwiyo | 2011 | ||
Armala | 2011 | ||
Malika | 2011 | ||
Tsaraba | 2011 | ||
Mutallab | 2011 | ||
Mai Zamani | 2011 | ||
Jaraba | 2011 | ||
Ke Duniya | 2011 | ||
Toron Giwa | 2011 | ||
Fisabilillahi | 2011 | ||
Muradi | 2011 | ||
Rai Da Buri | 2011 | ||
Ankwa | 2011 | ||
'Yan Mata | 2010 | ||
Mai Ladabi | 2010 | ||
Sarauta | 2010 | ||
Kukan Zaki (the Lion’s Cry) | 2010 | ||
Balaraba | 2010 | ||
Ladidin Baba | 2010 | ||
Dan Sarki | 2010 | ||
Sai Wata Rana | 2010 | ||
Wasila | 2010 | ||
Artabu (A Mazauna) | 2009 | ||
Dijangala | 2008 | ||
Hafsah | 2007 | ||
Bana Bakwai | 2007 | ||
Sabon Sarki | 2006 | ||
Jamhuriya | 2005 | ||
Taurari | 2005 | ||
Gwamnati | 2003 | ||
zero hour | 2020 |
Shekara | Suna | Matsayi | Salo | Kamfanin daya shirya |
---|---|---|---|---|
2007 | Sitanda | Jarumi | Wasa | |
2011 | Carbin Kwai | Jarumi | Wasa | |
2012 | Madubin Dubawa | Jarumi | Wasa | |
2012 | Last Flight to Abuja | Jarumi | Wasa | Nollywood Film Factory |
2013 | Blood and Henna | Jarumi | Wasa | Newage Networks |
2013 | Confusion Na Wa | Jarumi | Was | Cinema KpataKpata |
2013 | Wani Hanin | Jarumi | Wasa | |
2014 | Matan Gida | Jarumi | Wasa | |
2015 | Jinin Jikina | Jarumi | Wasa | |
2016 | Nasibi | Jarumi | Wasa | |
2016 | Ojukokoro | Jarumi | Wasa | Singularity Media |
2017 | Banana Island Ghost | Jarumi | Wasa |
Ali Nuhu yana daga cikin jaruman fina-finan Hausa wadanda ke gaba-gaba wajen samun gagarumar nasarori a masana'antar ta Kannywood dama ta mutanen kudancin Najeriya wato Nollywood. Anan zamu kawo maku wasu daga cikin kyaututtukan da Ali Nuhu ya samu a harkar sa ta shirya fina-finai.[7][8]
Shekara | Kyauta | Rukuni | Sakamako |
---|---|---|---|
2005 | Arewa Films Award | Best Actor | |
2007 | 3rd Africa Movie Academy Awards | Best Upcoming Actor award | Nasara |
2008 | The Future Award | Best Actor | Nasara |
2011 | Zulu African Film Academy Awards | Best Actor (Indigenous) | |
2012 | 2012 Best of Nollywood Awards | Best Actor (Hausa) | Nasara |
2013 | 9th Africa Movie Academy Awards | Best Supporting Actor | Nasara |
2013 | 2013 Nigeria Entertainment Awards | Best Actor | Nasara |
2013 | 2013 Best of Nollywood Awards | Best Actor (Hausa) | Nasara |
2013 | City People Entertainment Awards | Kannywood Face | Nasara |
2014 | Kannywood Awards | Best Actor | Nasara |
2014 | Leadership Awards | Best Artiste | Nasara |
2014 | City People Entertainment Awards | Best Actor | Nasara |
2014 | City People Entertainment Awards | Kannywood Face | Nasara |
2014 | Arewa Music and Movie Awards | Pride of Kannywood | Nasara |
2014 | Arewa Music and Movie Awards | Best Actor (Popular) | Nasara |
2015 | 19th African Film Awards | Most Outstanding Actor | Nasara |
2015 | 2015 Best of Nollywood Award | Best Actor (Hausa) | Nasara |
2015 | 2015 Kannywood Awards | Best Actor (Popular) | Nasara |
2015 | City People Entertainment Awards | Kannywood Personality | Nasara |
2016 | 2016 Best of Nollywood Awards | Best Actor (Hausa) | Nasara |
2016 | Arewa Music and Movie Awards | Best Actor | Nasara |
2016 | Kannywood Awards | Best Actor | Nasara |
2016 | City People Entertainment Awards | Kannywood Face | Nasara |
2016 | Arewa Creative Industry Awards | Entertainment Award | Nasara |
2016 | Wazobia FM’s COWA Awards | Excellent Entertainer | Nasara |
2017 | Northern Nigeria Peace Awards | Best Actor | Nasara |
2017 | City People Entertainment Awards | Kannywood Face | Nasara |
2017 | City People Entertainment Awards | Best Actor | Nasara |
2017 | 2017 Best of Nollywood Awards | Special Recognition Award | An dakatar |
Ali Nuhu