Amsatou Sow Sidibé | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Dakar, 14 Oktoba 1953 (71 shekaru) |
ƙasa | Senegal |
Karatu | |
Makaranta | Panthéon-Assas University Paris (en) doctorate (en) : Doka, Kimiyyar siyasa |
Thesis director | Jacques Foyer (mul) |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa da Malami |
Employers | Université Cheikh Anta Diop (en) |
Kyaututtuka |
Amsatou Sow Sidibé (an haife ta a shekara ta 1953) Malama ce, lauya kuma 'yar siyasa daga Senegal. A shekarar 2012, ita ce mace ta farko da ta tsaya takarar shugabancin ƙasar.[1] Sidibé farfesa ce a fannin shari'a a Jami'ar Cheikh Anta Diop (Jami'ar Dakar), inda take aiki a matsayin darekta na Cibiyar 'Yancin Ɗan Adam da Zaman Lafiya.[2][3] Ta kuma kafa kuma ta yi aiki a matsayin shugabar kungiyar ci gaban Matan Afirka (RAFET), da ke Dakar.[4]
A cikin ayyukanta daban-daban, Sidibé ta bayar da shawarwarin diflomasiyya game da lafiyar mata, ilimi da daidaiton jinsi, ta taimaka wajen tsara dokoki game da cin zarafin mata da kuma tsara dokar daidaita jinsi ta Senegal a shekarar 2010, wanda ke buƙatar jam'iyyun siyasa a zaɓukan cikin gida da na ƙasa don samun mata a lokaci guda akalla rabin 'yan takararsu. Sidibé ta ce, "Mata suna magana game da daidaito a ko'ina, har ma a cikin daji,"[4] kuma ta ce, "Suna buƙatar kasancewa a matakin mafi girma don yanke shawara; wannan yana da mahimmanci."[5]
Sidibé ta halarci Jami'ar Paris II, inda ta sami digiri na uku a fannin shari'a da kimiyyar siyasa.[6]