Angèle Diabang Brener | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Dakar, 1979 (44/45 shekaru) |
ƙasa | Senegal |
Karatu | |
Harsuna | Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | darakta, mai tsara fim da marubin wasannin kwaykwayo |
Muhimman ayyuka |
Q126718832 Q3319846 Yandé Codou, la griotte de Senghor Q19544199 Q126718944 Q126719057 |
IMDb | nm2687886 |
Angèle Diabang Brener marubuciya ce ta ƙasar Senegal, darekta kuma mai shirya fina-finai.[1]
An haifi Angéle Diabang Brener a Dakar a shekara ta 1979. Kwarewarta da iliminta a harkar fina-finai ya gudana a Dakar a cibiyar Média Center de Dakar, daga baya a makarantar shirya fina-finai ta ƙasar Faransa La Fémis a birnin Paris, sannan kuma a fitaccen Filmakademie Baden-Württemberg a Jamus.
Ta fara aikinta a matsayin editar fina-finai sannan a shekarar 2005 ta ba da umarnin fim ɗin ta na farko, wani shirin da ya shafi ka'idojin kyawun matan Senegal mai suna "Mon beau sourire".[2][3] Ita ce ke tafiyar da kamfanin shirya fina-finai na Karoninka wanda ya shahara wajen yin fina-ffinai sama da ggoma sha bbiyu. [2]