Barbara Okereke | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1991 (32/33 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | entrepreneur (en) , baker (en) da cake designer (en) |
Barbara Okereke (an haife ta a shekara ta 1991) ƴar asalin Nijeriya nc mai tsara kek kuma ƴar kasuwa, wadda ta kafa da manajan darakta na Oven Secret Limited. A shekarar 2019 an saka ta a cikin jerin sunayen '30 kasa da shekaru 30 'na Forbes a Afirka . [1]
Barbara Okereke tana da digiri a fannin Injiniyan lantarki daga Jami’ar Jihar Anambra, da kuma MBA a fannin Man Fetur da Gas a Jami’ar Coventry . Ta koyi ƙirar kek a makarantar girke-girke na Cake a Greenwich, London . [2] [3] A shekarar 2015 Okereke ta fara kasuwancin burodin kanta a Fatakwal . [4] Ta ƙirƙiri ƙirar kek fiye da dubu, kuma an horar da sama da ɗalibai ɗari biyar a zahiri da kuma layi.
Forbes ta haɗa da Okereke, lokacin tana da shekaru 28, a cikin jerin sunayensu na 2019 na mutane 30 'yan kasa da shekaru 30 da za su kalla a Afirka . [5] A shekarar 2020 jaridar The Guardian ta saka ta a cikin jerin sunayen mata 100 masu kwazo a Najeriya . [6]