Claudia Salas | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Madrid (mul) , 23 ga Yuli, 1994 (30 shekaru) |
ƙasa | Ispaniya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm10273610 |
Claudia Calvo Salas (an haife ta ne a ranar 23 ga watan Yuli a shekarar 1994), wacce aka fi sani da Claudia Salas yar wasan kwaikwayo ce ta kasar Spaniya. Ta sami sananne saboda aikinta na Rebe a cikin Elite.
Claudia Calvo Salas an haife ta ne a birnin Madrid a ranar 23 ga watan Yuli a shekarar 1994.[1][2] Ta yi karatun wasan kwaikwayo a Makarantar Drama ta Arte4 a Madrid.[1] Damarta ta farko ta talabijin ta kasance ƙaramar rawa a cikin wasan opera ta sabulu Seis hermanas.[3] Ta taka rawa a matsayin Rebe a cikin zango na biyu na shirin Elite,[4] Hakazalika ta fito a choni,[5], wanda ya haifar da cigaba bayan an saki fim din a shekarar 2019.[4] Sannan ta fito a matsayin Escalante a zango na biyu na shirin La peste,[6] shirin wasan kwaikwayo da yasa ta samu kyautar Gwarzuwar sabuwar yar wasan kwaikwayo a bikin bayar da kyaututtukan na 29th Actors and Actresses Union Awards.[7] Harwayau ta dawo a matsayin Rebe a zango na uku, hudu. da biyar na shirin Elite kuma sun fito a cikin fim mai ban tsoro na shekarar 2022, mai suna Piggy.[8]
A cikin Fabrairu 2022, ta yi haɗin-gwiwa tare da Ricardo Gómez, Elisabet Casanovas da Àlex Monner babban jarumi a shirin fim mai dogon zango na The Route, Wani dan gajeren fim mai dogon zango game da jerin lokaci game da, Samfuri:Ill.[9]
Shekara | Suna | Matsayi | Notes | Samfuri:Abbrv |
---|---|---|---|---|
2019–22 | Élite | Rebeka "Rebe" Parrilla | Main (seasons 2–5) | [10] |
2019 | La peste | Escalante | Main (season 2) | [11] |
2022 | Cerdita (Piggy) | Maca | Film | [12] |
2022 | La ruta (The Route) | Toni | Main | [13] |
2023 | Las pelotaris 1926 | Idoia | Main | [14] |
Shekara | Lambar yabo | Iri | Aiki | Sakamako | Ref. |
---|---|---|---|---|---|
2020 | 29th Actors and Actresses Union Awards | Best New Actress | La peste | Ayyanawa | [15][16] |
2023 | 10th Feroz Awards | Best Main Actress in a Series | The Route | Lashewa | [17] |