Elisabeth Ibarra | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Azkoitia (en) , 29 ga Yuni, 1981 (43 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Ispaniya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Yaren Sifen Basque (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga tsakiya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 1.61 m | ||||||||||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm7439749 |
Elisabeth “Eli” Ibarra Rabancho (an haife ta a ranar 29 ga watan Yuni a shekara ta, 1981) ‘yar wasan ƙwallon ƙafa ta ƙasar Sipaniya ce mai ritaya wacce ta taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya ko mai tsaron baya. Ta buga wasan ƙwallon ƙafa a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Eibartarrak FT daga shekarar, 1995 zuwa 2002 da kuma ƙungiyar Superliga/Pimera División Athletic Bilbao daga shekarar, 2002 zuwa 2017.[1] Ta buga wasanni 44 a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta ƙasar Sipaniya inda ta zura kwallaye biyu.[1]
Ibarra ta rike rikodin mafi yawan buga wasa a rukunin farko na mata na Athletic Bilbao (413)[1] har sai da tsohuwar abokiyar wasan Erika Vázquez ta wuce ta a shekara ta, 2022.[2] Kwallaye 111 da ta ci a duk wasannin da ta buga sun sanya ta zama ta uku mafi yawan zura kwallaye a duk lokacin.[1] Ita ce kuma 'yar wasa daya tilo da ta taka rawa a dukkan gasar lig guda biyar da kungiyar ta lashe.[1]
Ibarra ta fara buga kwallon ƙafa tun tana shekara 13.[3] Ta yi wasa a Eibartarrak FT (yanzu SD Eibar) tsawon yanayi bakwai, daga shekarun 1995 zuwa 2002,[4] kafin ta shiga sabuwar kungiyar mata ta Athletic Bilbao a lokacin rani na 2002 zuwa 2003 Superliga kakar mata.[1][5] Lokacin da ta fara isa kulob din, ta zabi riga mai lamba 17, don girmama tsohon dan wasan Athletic Joseba Etxeberria.[4] Ta fara wasanta na farko a wasan da ta yi nasara da Torrejón da ci 7–1 a Lezama Facilities, a wani wasa na farko da kungiyar mata ta Athletic ta buga.[4]
Ibarra ta zura kwallo a wasanni biyu na farko na Athletic a gasar cin shekara ta, kofin mata ta UEFA. A cikin watan Disamba shekara ta, 2012, ta buga wasanta na 300 ga Athletic.[5] A cikin shekarar, 2016, ta lashe gasar lig ta biyar tare da Athletic kuma ta amince ta ci gaba da zama a kulob din na tsawon shekara guda.[6]
A watan Mayun 2017, tana da shekaru 35, ta sanar da yin murabus daga wasan kwallon kafa.[7][8] Ta buga wasanni 413 a Athletic Bilbao - 367 a gasar, 32 a Copa de la Reina, da 14 a gasar zakarun Turai.[1] Ita ce ta uku mafi yawan zura kwallaye a kulob din, bayan Erika Vázquez da Nekane Díez, da kwallaye 111; daga cikin 104 sun zo a gasar, biyar a Copa de la Reina, biyu kuma a gasar zakarun Turai.[8]
Ibarra ta kasance memba a cikin tawagar kasar Spain,[9] inda Ignacio Quereda ya tura ta a matsayin mai tsaron baya na hagu.[10] Ta kasance cikin 'yan wasan Spain da za su fafata a gasar cin kofin mata ta UEFA Euro 2013 a Sweden[11] da kuma gasar cin kofin duniya ta mata ta FIFA ta 2015 a Canada.
No. | Kwanan wata | Wuri | Abokin hamayya | Ci | Sakamako | Gasa | Manazarta |
---|---|---|---|---|---|---|---|
1 | 24 ga Yuni 2010 | Estadio Municipal de La Albuera, Segovia, Spain | Malta | 3–0 | 9–0 | Cancantar FIFA shiga gasar cin kofin duniya ta 2011 | [12] |
2 | 7–0 |
Athletic Bilbao