Fatoumata Coulibaly | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Bamako, 1950s (65/75 shekaru) |
ƙasa | Mali |
Karatu | |
Harsuna |
Faransanci Harshen Bambara |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi, darakta, gwagwarmaya da ɗan jarida |
IMDb | nm0183406 |
Fatoumata Coulibaly ta kasance yar shirin fim din ƙasar Mali ce, darekta, yar'jarida, kuma mai kare hakkin dan'adam, musamman akan gudanar da kaciyar mata (FGM).
Fatoumata Coulibaly ta fito ne daga gidan mawaka, kuma kakarta Bazéko Traoré mawakiya ce a yankin Sikasso, inda Coulibaly take daga nan.[1]
Coulibaly ta fara aikin ta n'a farko ne amatsayin ma'aikataciyar jarida a radiyo, mai gabatarwa a Mali, kafin ta samu tunanin fara wasa, sannan ta tafi dan taga darekta Ousmane Sow, wanda ya name ta da tayi kokarin rubuta tunanin ta amatsayin rubutun fim, kamar yadda Cheick Oumar Sissoko yayi.[1]
Coulibaly ta fara jan hankulan duniya ne taré da matakin ta acikin fim ɗin shekarar 1997 N'Golo dit Papa.[2]
Coulibaly ta fito a mataki mai muhimmanci acikin fim ɗin 2004 Moolaadé daga marubuci kuma darekta dan Senegal ɗin nan Ousmane Sembène. Coulibaly ta fito amatsayin Collé Gallo Ardo Sy, macen aure ta biyu cikin mata uku a wurin mijinsu, a wani kauye a kasar Burkina Faso, wacce ke amfani da moolaadé ("magical protection") dan kokarin kare yara mata daga kaciyar mata (FGM).[3] Coulibaly herself has been a victim of female genital mutilation.[4] Mai sukan nan Roger Ebert ya ba auna fim din da tauraro uku (cikin hudu), da rubuta "for me the best film at Cannes 2004, a story vibrating with urgency and life. It makes a powerful statement and at the same time contains humor, charm and astonishing visual beauty".[5] Coulibaly ta lashe kyautar Best Actress award Dan matakin ta acikin fim din Collé, a Cinemanila International Film Festival a 2005.[3] Wannan fim din ya taka rawar gani sosai a wurin fadada wayar dakai dangane da wider kaciyar mata FGM, Kuma Coulibaly ta cigaba da wayar da kai tun wannan lokacin.[6] Gangamin ta akan FGM an fitar da su amatsayin fim Africa on the Move: The Power of Song (2010).[7][8]
Coulibaly ta fito acikin fina-finai da dama, shirye-shiryen telebijin da wasu wasanni.[1]
Har a 2016, Coulibaly tana aiki a Office de radiodiffusion télévision du Mali (Office of Broadcasting Television of Mali) (ORTM).[1]