![]() | |||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||
Haihuwa | Johannesburg, 13 Mayu 1993 (31 shekaru) | ||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||
|
Fortune Makaringe (an haife shi a ranar 13 ga watan Mayu 1993) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Afirka ta Kudu wanda ke taka leda a matsayin ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Orlando Pirates ta Kudu. Yana kuma buga wa tawagar kwallon kafar Afirka ta Kudu kwallo. Ya taba bugawa Maritzburg United wasa a shekarun baya.[1]
An haife shi a Johannesburg,[2] Makaringe ya fara aikinsa a Moroka Swallows kafin ya koma Maritzburg United.[3] Makaringe ya sanya hannu a Orlando Pirates a lokacin rani na 2019.[4][5]
Makaringe ya buga wasansa na farko a [{Afirka ta Kudu]] a ranar 3 ga watan Yuni 2018 a wasan da suka tashi 0-0 da Madagascar, ko da yake Afirka ta Kudu ta yi rashin nasara da ci 4-3 a bugun fenareti.[6] Ya kasance yana cikin jerin ‘yan wasa 28 na farko da kasar Afrika ta Kudu za ta buga a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2019 amma ba ya cikin tawagar ‘yan wasa 23 na karshe.[7]