Kawu Peto Dukku | |||
---|---|---|---|
5 ga Yuni, 2007 - 6 ga Yuni, 2011 District: Gombe North | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Jihar Gombe, 14 ga Janairu, 1958 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | 2 ga Afirilu, 2010 | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | Peoples Democratic Party |
Kawu Peto Dukku sha hudu ga watan janairun shekara dubu daya da dari tara da hamsin da takwas - biyu ga watan afrelu a shekara ta dubu biyu da goma (14 ga watan January a shekarar 1958 – 2 gawat April a shekara ta 2010) an zabe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa a jihar Gombe, Nigeria, wanda ya karbi mulki a ranar 29 ga watan Mayu a shekara ta 2007. Ya kasance dan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
An haifi Dukku a ranar 14 ga watan Janairun shekara ta 1958 kuma ya sami diploma na farko a fannin harkokin kasuwanci .
Ya fara aikinsa a matsayin malamin makaranta. Daga baya ya shiga kamfanin mai na Goal Star da ke Maiduguri . An zabe shi dan majalisar dokokin jihar Gombe a shekarar 1999 kuma an sake zaben shi a shekarar 2003, lokacin da aka nada shi kakakin majalisar.
Bayan an zabe Dukku a matsayin dan majalisar dattawa a shekarar 2007, an nada Dukku matsayin mataimakin shugaban kwamitin majalisar dattawa kan jihohi da kananan hukumomi. An kuma nada shi mamba a kwamitin majalisar dattawa kan harkokin jiragen sama da wasanni. A cikin tantancewar tsakiyar wa’adi na Sanatoci a watan Mayun shekara ta 2009, ThisDay ya lura cewa bai dauki nauyin wani kudiri ba, amma ya dauki nauyin kudiri bakwai, ya ba da gudummawar muhawara a zauren majalisa kuma yana aiki a cikin aikin kwamiti. Wata majiya ta bayyana shi a matsayin Sanata mai shiru wanda ba kasafai yayi magana a zauren majalisar dattawa ba. [1]
Dukku ya rasu a Kaduna bayan gajeriyar jinya a ranar 2 ga watan Afrilu a shekara ta 2010. Ya bar ‘ya’ya shida, mata uku da tsowa uwa guda daya.
<ref>
tag; no text was provided for refs named vang679