![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | 1 Satumba 1939 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | 2 Nuwamba, 2012 |
Karatu | |
Makaranta | Kwalejin Barewa |
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | soja |
Digiri | Janar |
Mohammed Shuwa (An haife shi 1 ga Satumban shekarar 1939 - ya rasu 2 ga Nuwamban shekarata 2012) ya kasance Manjo Janar na Sojan Nijeriya kuma shi ne Babban Janar na farko na Kwamandan Runduna ta 1 ta Sojojin Nijeriya. Shuwa ya shugabanci runduna ta 1 ta sojojin Najeriya a lokacin yakin basasar Najeriya. Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kashe shi a Maiduguri a ranar 2 ga Nuwamban shekarar 2012.[1]
An haifi Shuwa a garin Masharte na jihar Borno a ranar 1 ga watan Satumban shekarata 1939. Ya halarci makarantar firamare ta Kala (1946-1947), Bama Central Elementary School (1948-1950), Bornu Middle School (1950-1952), da kuma Barewa College, Zaria don karatun sakandare (1952-1957).[2] Ya kasance abokin karatu tare da Gen. Murtala Muhammed a Barewa da kuma cibiyoyin soja da suka biyo baya. Tare da Murtala Muhammed da wasu irin su Illiya Bisalla, da Ibrahim Haruna, Shuwa ya shiga aikin sojan Najeriya a ranar 19 ga Satumba, 1958[3] kuma ya bi karatun horonsa na farko a Makarantar Koyon Musamman ta Jami'an Regular da ke Teshie, Ghana.[4] Ya karɓi kwamishininsa a matsayin Laftana na 2 a watan Yulin 1961 bayan kammala horar da jami'ai a Royal Military Academy Sandhurst .
Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne suka kashe Gen. Shuwa a gidansa da ke Maiduguri a ranar 2 ga watan Nuwamban, 2012.[5]
|url=
(help)