Jaridar This DayJarida ce ta ƙasar Najeriya. Ita ce babbar jaridar kamfanin, Leaders & Company Ltd kuma an fara buga ta a ranar 22 ga watan Janairu 1995. Hedikwatar ta na a Apapa, jihar Legas.[1]Nduka Obaigbena, shugaba kuma babban editan ƙungiyar This Day Media Group da Arise News ne ya kafa ta.
This Day memba ce ta Kamfanin Dillancin Labarai na Belt and Road.[2] Tun daga shekarar 2014, ta ci gaba da ƙulla alaƙa da ofishin jakadancin ƙasar Sin.[3]
A baya dai an soki mawallafin jaridar This DayNduka Obaigbena da rashin biyan ma’aikatan jaridar da kuma masu kawo kayayyaki.[4]
A shekarar 2001, wasu editoci da dama sun tsallake rijiya da baya a wani hatsarin jirgin sama a filin jirgin Maiduguri da ke Arewa maso Gabashin Najeriya.[5][6]
A shekarar 2012 ne aka kai wa, wa su ofisoshin Jaridar harin bom a cikin mota, a Abuja babban birnin ƙasar, da kuma Kaduna, harin ƙuna baƙin wake da aka kai da wasu motoci da ake kyautata zaton ƙungiyar ta’addanci ta Boko Haram ce ke da alhakin kai Hara-haren.[7][8]
Wanda ya kafa jaridar, Nduka Obaigbena ya yi gudun hijira a Landan a shekarar 1998, kafin ya dawo Najeriya.[9]
↑Batchelor, Kathryn; Zhang, Xiaoling, eds. (2017-06-26). "Newspaper coverage of China's engagement with Nigeria: Partner or predator?". China-Africa Relations: Building Images through Cultural Cooperation, Media Representation and Communication (in Turanci) (1 ed.). Routledge. doi:10.4324/9781315229096-10. ISBN978-1-315-22909-6.