![]() | |
---|---|
![]() | |
Rayuwa | |
Haihuwa | Malabo, 24 ga Afirilu, 1931 |
ƙasa | Gini Ikwatoriya |
Mutuwa | Malabo, 10 Oktoba 2019 |
Karatu | |
Makaranta |
University of Barcelona (en) ![]() |
Sana'a | |
Sana'a |
ɗan siyasa, marubuci da linguist (en) ![]() |
Employers |
University of Alcalá (en) ![]() National University of Equatorial Guinea (en) ![]() |
Mamba |
Academia Ecuatoguineana de la Lengua Española (en) ![]() Royal Spanish Academy (en) ![]() |
Trinidad Morgades Besari (24 Afrilu 1931 - 10 Oktoba 2019) marubuciyar Equatorial Guinea ce, Malama kuma jami'a ce ta diflomasiyya. Ita ce macen Equatoguine ta farko da ta sami karatun a fannin ilimi a jami'a.[1]
An haifi Morgades Besari a Santa Isabel (yanzu Malabo ) a cikin shekarar 1931.[2] She attended school in the Canary Islands and Barcelona, Spain. She graduated from the University of Barcelona in 1958 with a degree in philosophy and arts,[2] Ta halarci makaranta a Canary Islands da Barcelona, Spain. Ta kammala karatu daga Jami'ar Barcelona a shekara ta 1958 tare da digiri a falsafa da fasaha, ta zama mace ta farko ta Equatoguine da ta sami ilimin jami'a.[3]
A shekara ta 1959, Morgades Besari ta zama farfesa a fannin Harshe da Adabi a Makarantar Koyarwa ta Ma’aikatar Santa Isabel da ke Malabo. Ta halarci taron WHO a Addis Ababa a shekara ta 1964 kuma an naɗa ta Darakta a Cibiyar Cardenal Cisneros, Jami'ar Alcalá a shekara ta 1965.[2]
Bayan samun 'yancin kai na ƙasar Equatorial Guinea, an naɗa Morgades Besari a matsayin sakatariyar farko na ofishin jakadanci a birnin Lagos na Najeriya a shekarar 1968. A cikin shekarar 1971, an naɗa ta mai kula da al'adu a ofishin jakadanci a Addis Ababa.
Morgades Besari ta koma Spain a shekara ta 1973 kuma gwamnati ta naɗa ta a matsayin malamat adabi a Kwalejin Mishan na Franciscan da ke Tetouan, Maroko. Ta zama Shugabar Turanci da Adabi a Instituto Reyes Catolicos a Vélez-Málaga a cikin shekarar 1975. Besari ta koma Equatorial Guinea a shekarar 1986 kuma an naɗa ta Sakatariya Janar na Jami'ar Ilimi ta Ƙasa , tana koyarwa a ofishin jakadancin Amurka a Malabo. An naɗa ta Babbar Sakatariya na Kwamitin Bincike na Kimiyya na Equatorial Guinea a shekara ta 1988 da kuma Daraktar Makarantar Noma ta Ƙasa a shekara ta 1992.
Morgades Besari ta zama darektar jaridar El Correo Guineoecuatoriano a shekara ta 2000 kuma an zaɓe ta shugabar kungiyar 'yan jarida ta Equatorial Guinea a shekara ta 2003.[4] Ta rubuta kuma ta ƙaddamar da wani aikin wasan kwaikwayo mai suna Antígona, sake fasalin Sophocles 'Antigone.[2][5][6] A shekara ta 2005, an naɗa ta mataimakiyar shugabar jami'ar ƙasar Equatorial Guinea. Ta bar mukamintaa a cikin shekara ta 2010 lokacin da aka naɗa ta wakiliyar jami'ar Royal Spanish Academy . Ta haɗa kai da NGO Macoelanba don samar da tallafin karatu ga ɗalibai mata.
Besari ta auri Samuel Ebuka tun a shekarar 1965. Ta mutu a ranar 10 ga watan Oktoba 2019 a Malabo. Ta bar mace da namiji.
<ref>
tag; no text was provided for refs named homage
|s2cid=
value (help).