![]() | |
---|---|
submarine communications cable (en) ![]() | |
Bayanai | |
Farawa | 2011 |
GLO-1 kebul ne na sadarwa na ƙarƙashin ruwa, na ( Globacom-1 ). kebul ɗin da ke gaɓar tekun yammacin Afirka an jawo shine ta cikin ruwa a tsakanin Najeriya da Birtaniya, kuma kebul ɗin mallakar kamfanin sadarwa ne, na Globacom a Najeriya.
Kebul na ƙarƙashin tekun na da tsawon kilomita 9,800, kuma ya fara aiki a shekara ta 2011 tare da samar da ƙaramin ƙarfin kimanin 640 Gbit/s.
Aikin kamfanin Globacom, ne na 2 mafi girma a Najeriya a fannin sadarwa, ana tallata jimillar ƙarfin tsarin a matsayin 2.5 Tbit/s. An tsara jawo kebul ɗin izuwa Ghana a cikin watan Afrilu, 2011.[1]
Manyan wuraren tashoshin kebul na kamfanin sune:
A cikin Fabrairu 2018, The Sunday Times ta ruwaito cewa kayayyakin da Burtaniya ta kai a wuraren Apollo, GLO-1 da Europe India Gateway an samu kusan gaba ɗayan kayan ba tare da kula da su ba. Wakilin nasu ya isa harabar ba tare da fuskantar ƙalubale ba, inda ya tarar da kofar dakin janareta a buɗe aka barshi a wajen. Kamfanin Vodafone, wanda ke kula da wurin, ya ce bai kai kayan aiki masu mahimmanci ba kuma "ba zai iya katse aikin ginin ba."[2]
Jerin kebul na sadarwa na ƙarƙashin teku a duniya
Tsarin kebul mai guda ɗaya daga yammacin gabar tekun Afirka sun haɗa da:
|url=
(help)